Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A cikin makon nan ne fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Real Madrid, Karim Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or ta Gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta duniya na 2022, yayin bikin da ya gudana a birnin Paris, inda ya gaji Lionel Messi wanda ya lashe kyautar a bara.
A shekarar bana dai, Paris babban birnin Faransa ya zama na musamman ga ɗan wasan gaban na Real Madrid, domin kuwa a nan ne, suka lashe kofin gasar Zakarun Turai karo na 14, bayan doke Liverpool da 1-0 a watannin baya.
Ƙididdiga ta nuna cewar, sau goma sha biyu aka baiwa ’yan wasan Real Madrid kyautar Ballon d’Or, wanda ya yi daidai da adadin da ’yan wasan Barcelona suka samu.
Tsofaffin ’yan wasan Real Madrid da suka samu kyautar gwarzon ɗan wasan a baya sun haɗa da Alfredo Di Stefano da Raymond Kopa da Luis Figo da Ronaldo Nazario da Fabio Cannavaro da Cristiano Ronaldo da kuma Luka Modric.
Benzema wanda ya taka rawar gani a gasar zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce, shi ne ɗan wasan Faransa na farko da ya lashe kyautar ta Ballon d’Or tun bayan Zidane a shekarar 1998.
Sadio Mane ne ya zo na biyu, sai Kevin de Bruyne na uku, yayin da Robert Lewandowski ya zo na huxu.
Courtois ya yi wa masu tsaron raga zarra, Mane ya lashe kyauta ta musamman
A ɓangaren masu tsaron raga kuwa, golan Real Madrid Thibaut Courtois ne ya lashe kyautar zama Gwarzo, la’akari da gagarumar gudunmawar da ya baiwa ƙungiyarsa yayin wasanni mafiya hatsari da ta buga a kakar wasan da ta gabata, musamman yayin karawa da Liverpool a wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai.
Kyauta ta musamman don karrama wanda ya fi gudanar da ayyukan jin qai, an miƙa ta ne ga ɗan wasan gaban Bayern Munich da Senegal Sadio Mane, bisa irin gudun mowar da ya ke bayarwa ga rayuwar jama’a.
Ɗan wasan tsakiya na Barcelona da Spain Gavi, ne ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi hazaka.
Mancester City ce gwarzuwar ƙungiya ta shekarar 2022;
Wannan ya dogara ne akan City da ke da mafi yawan ’yan wasan sunayen su ya fito a ɓangarori daban-daban na wannan kyauta.
Liverpool ke biye mata a mataki na biyu, sai Real Madrid da ta kasance a matsayi na uku.