Shugabanni ne ya kamata su bada misali wajen bin umarnin kotu – Alh. Hamisu Ƙarami

Manhaja logo

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

An bayana cewa babu wanda ya kamata ya girmama doka da binta kamar shugabanni, domin aikin shugaba ne ya zama babban misali ga talaka mai ƙaramin ƙarfi wanda ba shi da wami zaɓi sai dai ya bi doka ko yana so ko ba ya so, wannan shi ne abin da doka ta sani.

Alhaji Hamisu Ƙarami, wani matashi ne mai fashin baƙi a kan al’amuran yau da kullum, ya bayana haka ne a lokacin da yake hira da ‘yan jarida a ofishinsa dake Kano a ranar Lahadi da ta gabata.

Ya ce zargin da aka yi wa wasu hukumomi a Kano na ƙin bin umarnin kotu da ta hana a rushe shaguna kimanin 3,800 a kasuwar Banfai da cewa abin takaici ne a ce hukumomi suna irin wannan, “domin dai kowa zaman doka ya ke yi kuma duk ranar da aka ce babu doka to fa abu ya vaci Allah ya kiyaye.”

Har ila yau ya yi kira da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan ya tsaya tsayin daka wajen ganin an hana yin abinda ya savawa doka musamma da wasu suke amfani da sunan gwamnati suna ƙoƙarin ɓata mata suna, wanda kuma daga baya a cewarsa sai a ji gwamnan Kano bai sani ba kamar abubuwan da suka faru a kasuwar Kantin Kwari da sauran wurare na gini ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya ce akwai buƙatar gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike na gano duk wanda aka zalinta ko aka mai ba daidai ba a biya shi diyya domin hakan shi ne adalci kuma duk wani shugaba da ake yabo ko ake tunawa to ana yin haka ne sakamakon adalci da tausayi da ya nuna a zamanin mulkinsa.

wannan ne ya sa, “kullum ake tunawa da irinsu Sir Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato da irinsu Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Marigayi Janar Murtala Muhammad wanda ya yi mulki kwana 200 tak amma har yanzu ana tina alkairinsa, da irin su Malam Aminu Kano, Alhaji Abubakar Rimi, Alhaji Audu Bako da sauransu duk alkairi ne da suka yi ya sa ake tunasu da yi musu addu’a a koyaushe.”

A ƙarshe Alhaji Hamisu Karami ya yi amfani da wannan dama wajen neman al’umma ta cigaba da addu’ar samun cigaban zaman lafiya a Kano da qasa baki ɗaya, inda kuma ya buƙaci matasa su guji bangar siyasa da kuma shan kayan shaye-shaye ko razana al’umma da makamai a wannan lokaci na yaƙin neman zaɓe mai zuwa na 2023 a Nijeriya.