Daga ZAHARADDEEN ILIYASU a Kaduna
Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group ta gudanar da gagarumin taron Maulidin Manzon Allah (SAW) na watan Rabi’ul-Awwal na shekarar 1448/2026 a Kaduna, inda aka shafe tsawon dare ana gudanar da ibadu da shirye-shirye daban-daban domin ƙarfafa soyayya ga Manzon Allah (SAW) da kuma koyarwarsa.
Taron ya ƙunshi karatun Alƙur’ani, zikiri, rera yabo da salati ga Manzon Allah (SAW), gaisuwar sada zumunci, rabon kyaututtuka da takardun shaidar kammala haddace wasu littattafai, tare da gudanar da addu’o’i na musamman a ƙarshen taron.
A yayin taron, babban Shehin Zawiyyar, Shehu Isma’ila Umar Almaddah, ya gabatar da dogon wa’azi inda ya yi bayani kan muhimmancin murnar zagayowar lokacin haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) da nuna soyayya gare shi.
Ya bayyana watan Rabi’ul-Awwal a matsayin lokaci na tunawa da babbar ni’imar da Allah Ya yi wa duniya ta hanyar aiko ManzonSa a matsayin rahama ga dukkan halittu.
Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya kuma yi bayani kan ma’anar soyayya da nau’o’inta, yana mai jaddada cewa soyayya ta gaskiya ga Manzon Allah (SAW) ba ta tsaya kan furuci kawai ba, sai an haɗa ta da koyi da kyawawan halayensa.
Ya yi kira ga malamai da masu ilimi da su ƙara ƙoƙari wajen isar da saƙon Manzon Allah (SAW) ga al’umma, ba tare da takaita shi ga wata ƙabila, yare ko nahiya guda ba, domin Manzon Allah (SAW) ma’aiki ne ga dukkan halitta.
Haka kuma, Shehun ya jaddada muhimmancin haɗa ilimin addini da na zamani, yana mai kira ga al’umma, musamman matasa, da su dage wajen neman ilimi, samun ƙwarewa da wayewa domin samun ci gaba.
Ya kuma yi kira da a ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan al’umma, yana mai cewa abubuwan da suka haɗa mutane sun fi waɗanda suka raba su yawa.
Taron ya samu halartar wakilan al’umma daga wurare daban-daban, inda wasu daga cikinsu suka gabatar da saƙonnin gaisuwa da fatan alheri daga al’ummominsu cikin harsuna daban-daban, ciki har da Turanci, Faransanci, Larabci da Fulatanci.
Kamar yadda aka saba a irin wannan taro, an gudanar da karatuttuka daban-daban da suka haɗa da karatun Alƙur’ani da Tahni’a, zikiri, salati da yabon Manzon Allah (SAW).
A wani ɓangare na taron, an miƙa takardun shaida ga ɗaliban da suka samu nasarar haddace Diwani baki ɗaya, da waɗanda suka haddace Rihilolin Shehu Ibrahim baki ɗaya, da kuma masu haddar Goran Faila.
Haka kuma, Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya gabatar da zane-suna ga jariran da aka haifa, tare da yi musu addu’ar samun albarka, kyakkyawar rayuwa da makoma mai kyau.
An gudanar da addu’ar ƙarshe da misalin ƙarfe 5:30 na safe, inda aka yi addu’a ga Afirka da duniya baki ɗaya, tare da roƙon Allah Ya kawo zaman lafiya, tsaro, arziki da ci gaba.
Daga bisani aka gudanar da Sallar Asuba, tare da sauran addu’o’in da ake yi a ƙarshen taron Maulidin.
Taron ya kasance wata dama ta haɗa al’umma a kan soyayya ga Manzon Allah (SAW), murnar zagayowar lokacin haihuwarsa da kuma ƙarfafa gwiwar matasa da sauran al’umma wajen neman ilimi, zaman lafiya da haɗin kai.
