Yadda gwamnan Zamfara ya inganta harkokin kiwon lafiya a jihar

Daga BELLO A. BABAJI

Biyo bayan taɓarɓarewar harkar kiwon lafiya a Zamfara a shekarun baya, Gwamna Dauda Lawal ya shelanta dokar ta-ɓaci a ɓangaren jim-kaɗan da kama mulki a jihar.

A ƙoƙarinsa na inganta harkar lafiya, gwamnan ya fara ne a gyare-gyaren asibitoci da zamanantar da su da sanya kayayyakin aiki na zamani da kuma gina waɗansu asibitocin.

Acikin shekara guda ne rashin kula da asibitocin suka yi fama da shi ya zama tarihi inda aka ƙawata gine-ginensu da samar musu da ƙwararrun ma’aikata don amfanin al’umma a jihar.