Yadda gwamnatin tarayya ta raba mata sama da 1600 da larurar yoyon fitsari – NHIA

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Akwai mata sama da 1600 da aka yi wa aiki da ke fama da larurar yoyon fitsari a ƙarƙashin hukumar inshoran lafiya ta ƙasa na shirin aikin yoyon fitsari kyauta (FFP) da gwamnatin tarayya ke yi.

Dr Saka Agboola, shugaban sashen tabbatar da ingancin aiki na hukumar inshoran lafiya ta duniya (NHIA) ne ya tabbatar da hakan a cikin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Ilorin a ranar Litinin.

Agboola ya ce, manufar shirin gwamnatin tarayya ita ce yin tiyata kyauta da shigar da mata cikin tsarin inshorar lafiya.

“Gwamnatin Nijeriya ta fahimci cewa akwai ƙarancin cibiyoyin kula masu yoyon fitsari. Don haka, akwai buƙatar ƙara wasu guda 18 a faɗin ƙasar nan.

“Da wannan shiri, an yi wa mata 1600 da ke fama da yoyon fitsari,” ya bayyana.

Agboola ya ce, Nijeriya na son cimma rage yawan mata masu fama da yoyon fitsari 400,000 a Nijeriya don rage yawan mutuwar mata masu juna da jarirai.

NAN ta rawaito cewa yoyon fitsari wata larura ce da ta danganci huji da ake da ita a tsakanin gaɓoɓi guda biyu ko jakar ajiye fitsari da ba su da alaƙa da juna.

A cikin irin waɗannan larurori akwai hujin da ke faruwa tsakanin gaban ‘ya mace da kuma jakar ajiyar fitsari.

Wannan larura na faruwa ne sakamakon shafi tsawon lokaci ana naƙuda ko rashin samun cikakkiyar kulawar lafiya.

Agboola ya ce ƙasashe masu tasowa ne suka fi fama da wannan larura inda ake samun faruwar lamarin har kusan miliyan 1.

Ya kuma ƙara da cewa ta hanyar wannan shiri, an yi nasarar taimaka wa waɗanda ba su da ƙarfin samun kuɗi da yaye musu fama da raɗaɗi da ba su abinci da sufuri da kuma kuɗin da za su riƙe a hannu.

By ukarofi