Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin jihar Sakkwato ta ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa masu ɗaukar mutum 20 da rigunan kariya 2,000 a yankunan jihar da ke kusa da koguna.
Yayin ƙaddamar da aikin a garin Dundaye da ke yankin ƙaramar hukumar Wamako, gwamnan jihar Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa da ɗauki matakin ne da nufin kare lafiya da dukiyoyin al’ummomin jihar da ke rayuwa a kusa da koguna.
Gwamnan ya ce matakin zai taimaka wajen inganta lafiyar sufurin ruwa da nufin rage yawan hatsuran da ake yawan samu a kwale-kwale a gokuna da tafkunan jihar.
Ya ƙara da cewa sabbin jiragen za su taimaka wa manoma don zuwa gonakinsu, musamman a yanayin ambaliya.
Ahmad Aliyu ya ce a yau gwamnatinsa ta raba sabbin jiragen 20 da rigunan kariya 1,000 ga ƙananan hukumomi 10.
To sai dai gwamnan ya gargaɗi matuƙa sabbin jiragen ruwan su guji loda fasinjoji fiye da abin da aka ƙayyade wa jirage, yana mai cewa duk direban da ka samu da kauce wa dokar zai ɗanɗana kuɗarsa.
A shekarun baya-bayan nan ana yawaitar samun hatsarin kwale-kwale a kogunan Nijeriya, wani abu da masana ke alaƙantawa da rashin ingancin jiragen da ƙarancin rigunan kariya.
