Yadda jami’an tsaro suka gano ‘kaburbura’ 30 a wani otel a Anambra

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jami’an tsaro a jihar Anambra sun gano “kaburbura sama da 30 ” a wani otel da ke Oba, ƙaramar Hukumar Idemili ta Kudu a jihar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun gano kaburburan ne a ƙarshen mako bayan samun rahoto daga wani mazaunin yankin.

Ginin, wanda ke kan hanyar Onitsha-Owerri, an yi masa rijista da suna Udoka Golden Point Hotel and Suites, amma ya fi shahara da suna La Cruise Hotel.

Wani saƙon da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar Anambra a ɗ ya ce “otel ɗin yana da kaburbura sama da 30, a bene na ƙarshe tare da wuri na bauta”.

Onyeka Ibezim, mataimakin gwamna a jihar Anambra, ya jagoranci jami’an tsaro wajen rusa ginin a ranar Asabar.

Da ya ke magana da ‘yan jarida bayan sintirin, Ibezim ya ce babu gurbi ga aikata laifi a wannan jihar ta Kudu maso gabas.

By ukarofi