An zaɓi Rena Wakama a matsayin mafi ƙwarewar koci a gasar 2024 a birnin Paris bayan da ta jagoranci tawagar DTigress ta Nijeriya zuwa wasanni masu ban sha’awa a tarihin gasar ƙwallon kwando ta Olympics.
Nijeriya ta nuna bajinta bayan da ta doke Australia a ranar buɗe gasar, wanda shi ne karon farko da tagawar ta samu nasara a wasan rukuni.
Kwanaki kaɗan bayan haka, Nijeriya ta bai wa ƙasar Canada mamaki inda ta zama tawaga ta farko a nahiyar Afrika da ta samu nasara sau biyu a gasar, inda ta kuma yi tsayuwa tsayin daka wajen kare martabar ƙasarta.
Nasarar ta baiwa ‘yan matan Tigeri tikitin zuwa zagayen gaba, inda ta zama tawaga ta farko a Afirka a tarihi, maza ko mata, da za su taka leda a gasar Olympics ta wasan kusa da na ƙarshe.
Bajintar ta su ta ƙare a ƙarshe lokacin da Amurka ta doke su, amma duk da haka sun nuna cewa ko ba “kanwar lasa” ba ne har zuwa ƙarshe.
