Jami’ar UNIBEN tana binciken malami bisa cin zarafin ɗaliba

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Benin (UNIBEN) ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai binciki zargin cin zarafin da ake yi wa wani farfesar jami’ar.

Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da sakataren kwamitin binciken Barista B.D. Jonathan ya fitar.

Kwamitin ya buƙaci ma’aikata da ɗaliban da suke da bayanan da suka dace ko kuma sun fuskanci makamancin lamarin da ya shafi zargin da su fito su yi bayani.

A cewar sanarwar, “bayanan za su taimaka wa kwamitin wajen tabbatar da gudanar da sahihin bincike.

“Ku tabbata cewa za a kare ku, kuma duk bayanan za a bi da su da cikakken sirri.”

An tattaro cewa cibiyar ta ɗauki wannan matakin ne bayan wata da ta kammala karatun jami’ar ta shiga kafafen sada zumunta inda ta zargin malamin da neman ɗalibansa mata.

Tsohuwar ɗaliban jami’ar ta yi zargin cewa ta fuskanci cin zarafi a lokuta da dama daga farfesan lokacin da take karatun digiri na farko a jami’ar.

By ukarofi