Sojoji sun ceto mutum 59 daga nutsewa a ruwa a Ribas

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya ta ce ta yi asarar wani jami’i bayan ceto mutane 59 daga nutsewar ruwa a kogin Okpobo da ke jihar Ribas

Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Commodore A. Adams-Aliu, ya bayyana a wata sanarwa cewa a ranar 30 ga Yuli, 2024, sojojin ruwan Nijeriya sun samu kiran gaggawa daga Mɓ AMBIKA 4, wani jirgin ruwan da ke aiki a filin Okpobo da kwangilar da kamfanin Sterling Global Oil ta bayar.

Ya ce, sakamakon binciken ya nuna cewa jirgin na fuskantar barazanar nutsewa a kusa da mashigar kogin Okpobo, yankin da aka fi sani da tashin hankali a wannan lokaci, inda ya ƙara da cewa rundunar sojojin ruwa ta Nijeriya ta BONNY ta tura tawagar ceto da ta ƙunshi mutane 10 ɗauke da makamai a cikin jiragen ruwa, aaraashin jagorancin Jami’in Ayyuka na Base, Laftanar Kwamanda Gideon Yashim Gwaza, domin aikin ceto.

Ya ƙara da cewa, yunƙurin tunkarar jirgin da ke cikin mawuyacin hali ya zama aalubale saboda ƙarfin ruwa, inda aka ƙara turo wata tawagar jiragen ruwa uku domin ƙarfafa tawagar ceton.

A cewar sanarwar, an tura wani jirgin ruwa, Jirgin ruwan Nijeriya GONGOLA, jirage marasa matuƙa, da jirage masu saukar ungulu, da kuma wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin saman Nijeriya guda ɗaya domin gudanar da aikin ceto.

Ya ce, an kuɓutar da dukkan ma’aikatan jirgin 59 cikin nasara amma jami’in kula da ayyukan sansanin, Laftanar Kwamanda Gideon Yashim Gwaza ya rasu a yayin aiwatar da hakan.

By ukarofi