Yadda kwalliya ta biya kuɗin sabulu a shirin bunƙasa noma a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwalliya ta biya kuɗin sabulu a katafaren shirin nan na bunƙasa noma da kiwo na Jihar Kano, wanda aka yi wa laƙabi da KSDP, wanda shiri ne da yake samun tallafi daga Bankin Addinin Musulunci dake Ƙasar Saudi Arabiya.

Shirin na samar da hanyoyin da za a bunƙasa yawan abincin da ake nomawa a Jihar Kano ƙarƙashin ƙungiyar Sasakawa.

A wannan mako ne ƙungiyar ta gayyaci ‘yan jaridu domin nuna musu irin ayyukan da suka yi a wannan shekara da muke bankwana da ita. Da fari an bai wa ƙungiyar ta Sasakawa damar koyar da manoma maza da mata 112,000, to sai dai kuma har ƙungiyar ta samu nasarar koyar da manoma 114,950 kamar yadda shugaban shirin ya bayyana.  

Wannan ya haɗa da dabarun bunƙasa noma kama daga aikin gona, da yadda za a ajiye shi bayan girbi da kuma yadda za a ƙara masa daraja don samun gwaggwaɓar riba, ciki har da haɗa manoma da masu sayen kayan amfanin gona.

A nasu ɓangaren shugaban hukumar bunƙasa harkar noma ta jihar Kano (KNARDA) Dr. Junaidu Yakubu da shugaban shirin bunƙasa noman na wannan shirin, Malam Ibrahim Garba Gama sun nuna jin daɗin su da gamsuwa da yadda ƙungiyar ta Sasakawa take aiwatar da aikin da aka ɗora mata a cikin shirin na KSDP.

Shi kuwa mataimakin shugaban ƙungiyar ta Sasakawa Dr. Abdulhamid Gambo godiya ya yi ga Gwamnatin Jihar Kano da Bankin Addinin Musulunci dake Jidda a Saudi Arabiya da sauran hukumomin da suka tallafa bisa dama da aka bai wa ƙungiyar na shiga a dama da ita cikin shirin.

Manoma daban-daban da suka fito daga ƙananan hukumomin jihar nan sun bayyana gamsuwar su tare da tabbatar da irin ƙarin nasarar da suka samu.  

A garin Token da ke ƙaramar hukumar Warawa, wani manomi mai suna Mukhtar Garba, ya samu buhuna ɗari da uku a kadada ɗaya, ya ce sakamakon haka yanzu ya buɗe shagon sayar da kayan aikin gona a ƙauyen na su. Shi kuwa Sani Yakubu da ya yi nasa noman a ƙauyen Samawa da ke G/Malam, ya ce zai biya wa ‘yar uwar sa kuɗin aikin Hajji saboda gwaggwavar ribar da ya samu.

Ƙungiyoyin mata daban-daban ne suka amfana da tallafin kayan aiki na gyaran shinkafa tare da sanin hanyoyin yadda za su sarrafa shinkafa tayi daidai da wacce ake shigowa da ita daga waje duk a cikin shirin.

Manoma dai daban-daban sun bayyana godiyar su bisa tallafin da suka samu cikin wannan shiri, a ƙarshe sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara himma bisa tabbatuwar wannan shiri don sun ce ba shakka sun ga amfanin sa.