Sani Buhari Daura ya kwanta dama

Daga WAKILINMU

Allah Ya yi wa hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Sani Buhari Daura (Walin Daura) rasuwa.

Ɗan marigayin Abdulrasheed Daura ne ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa ga jaridar Daily Nigerian, yana mai cewa marigayin ya rasu ne da safiyar Lahadi a can ƙasar Dubai.

A halin rayuwarsa, Marigayi Daura shi ne shugaban kamfanoni da dama da ya kafa, da suka haɗa da kamfanin Bayajidda Nigerian Limited da Standard Construction Limited da Buhari Properties and Development Company da kuma kamfanin nan na Katsina Oil Mill.

Kamfaninsa na Standard Construction Limited shi ne ya gina fitaccen ginin nan da ake kira Ship House a Abuja wanda a yanzu Ma’aikatar Tsaro ke amfani da shi.

Alhaji Sani Buhari Daura ya bar duniya yana da shekaru 90 daidai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *