Farfesa Khalid ya ja kunnen malamai a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban hukumar ilmin bai ɗaya ta jihar Kebbi (SUPEB), Farfesa Suleman Khalid ya ja kunnen ma’aikata musamman malamai kan tsare aiki.

Ya yi wannan bayani ne jiya Alhamis da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Augie a cikin wani rangadi da ya ke na ganewa idonsa yadda aikin koyarwa a makarantun firamare ke tafiya a faɗin jihar.

Farfesa Suleman Khalid ya ce ya ziyarci yankunan Yola da Gobirawa, inda ya tabbatar wa malamai da cewa gwamnatin jihar Kebbi tana nan tana tsare-tsaren tabbatar da bai wa kowane malami haƙƙinsa, saboda haka ya kamata kowa ya tsare bakin aikinsa saboda gwamnati ba za ta lamunce wa duk wani malami da ke barin wajen aikinsa ba tare da wani takamaiman dalili ba.

Yanzu dai an gyara makarantu an kuma kai malamai da kayan aiki saboda haka babu wani dalilin rashin zuwa wajen aiki.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su kai yara makaranta domin samun ingantaccen ilmi musamman ko ba komai za a samu ilmin mu’amala wanda ko ba don mutum ya yi aikin gwamnati ba.

Ya ƙara da cewa neman ilmi wajibi ne ga kowane musulmi da musulma, saboda haka ba sai ƙananan yara ba kowa yana iya shiga makaranta, saboda yanzu haka gwamnati ta yi tanadi ƙwaƙƙwaran wajen harkar ilmi wanda a sanadiyyar haka aka farfaɗo da ilmin yaƙi da jahilci wanda yanzu haka yana samun karɓuwa wajen maza da mata, inda yanzu haka suna ci gaba da halartar cibiyoyi daban-daban a faɗin jihar.