Ya sayar da ɗansa, ya yi wa mahaifiyar ɗan ƙaryar ya mutu

Rundunar ’yan sanda a jihar Abia, ta kama wani ɗan shekara 40, Appolos Ndubuisi, bisa zargin sayar da ɗansa na miji kan kuɗi naira 350,000, bayan ya yaudari mahaifiyarsa da cewar ya mutu a lokacin haihuwa.

An tattaro cewa, Ndubuisi ya haɗa kai da wata Rose Godwin Chinweikpe, wacce ke da wajen karɓar haihuwa a garin Owoahia-Afor da ke yankin Obingwa, wajen sayar da jinjirin.

Rahotanni sun ce, matar Ndubuisi, Deborah Onukaogu ce ta haifi jinjirin wanda ya kasance bakwaini.

Da ta ke jawabi ga manema labarai a Umuahia, kwamishinar ’yan sandan jihar Abia, Janet Agbede, ta ce, Omukaogu ta ɗauki cikin Appolos Ndubuisi, ɗan asalin ƙauyen Umuariaga a yankin Ikwuano da ke jihar.

Kwamishinar ta bayyana cewa, Onukaogu ta sanar da ’yan sanda cewa, Ndubuisi bai cike sharuɗan da zai sa ta zamo matarsa ta sunna ba.

Sai dai kuma, an tattaro cewa, Onukaogu ta haifi da namiji a ranar 26 ga watan Yunin 2021 amma waɗanda ake zargin, Ndubuisi da Rose suka haɗa kai tare da ikirarin cewa yaron bakwaini ne.

Deborah ta sake ɗaukar Ndubuisi wanda ya nemi ta sake zuwa asibitin Rose don sake haihuwa a wajen.

Sakamakon zargi da ta ke game da bakwainin da aka ce ta haifa, sai Deborah ta shigar da ƙara ofishin ’yan sanda wanda ya yi sanadiyar kama mutanen biyu.