Yadda magungunan gargajiya ke jefa ’yan Nijeriya haɗari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aƙalla mutane 48 ne suka rasa rayukansu a Jihar Ondo bayan shan wani maganin gargajiya da aka fi sani da ‘agbo’, lamarin da ya sake jawo hankali kan haɗarin amfani da magungunan gargajiya ba tare da kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya ba.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar Hukumar Odigbo, inda sama da mutane 170 kuma suka kamu da rashin lafiya mai tsanani bayan shan gaurayen maganin, kamar yadda Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) da jami’an lafiya na jihar suka bayyana.

Mutanen da abin ya shafa sun fito daga al’ummomin Araromi-Obu, New Town, Odole, Okele, Orita Odigbo da Oniparaga.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a matsayin abin matuƙar tayar da hankali.

Ta ce, sama da mutane 40 sun mutu sakamakon shan gaurayen maganin gargajiya da aka sarrafa a gida, yayin da wasu da dama ke ci gaba da karɓar magani a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Owo da kuma Asibitin ƙwararru na Jihar Ondo.

Bayan faruwar lamarin, Shugaban ƙaramar Hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya sanya dokar hana sayarwa da shan dukkan nau’o’in barasa da ake sarrafawa a gida da kuma gaurayen magungunan gargajiya na cikin leda a yankin na tsawon wata guda.

Hukumar magungunan gargajiya ta ɗauki mataki:

Hukumar Kula da Masu Sana’ar Magungunan Gargajiya ta Jihar Ondo ta ce za ta fara gudanar da horaswa ga masu wannan sana’a domin inganta yadda suke sarrafa magungunansu.

Hukumar ta kuma bayyana cewa za ta wallafa jerin sunayen masu sayar da “agbo” da aka amince da su tare da lambobin rajistarsu, kamar yadda ake yi wa masu sayar da magungunan asibiti.

Sai dai abin da ya faru a Ondo ba shi ne karo na farko da shan irin waɗannan gaurayen magunguna ya haddasa mutuwar jama’a ba.

A shekarar 2023, Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa ta danganta mutuwar wasu mutane a Kano da wani gaurayen magani da ke ɗauke da sinadarin ethanol mai yawa.

Haka kuma a shekarar 2024, yara shida sun mutu a Jihar Sakkwato bayan sun sha maganin gargajiya domin neman maganin cutar kyanda.

Duk da irin waɗannan abubuwan, amfani da magungunan gargajiya na ci gaba da yaɗuwa a sassan ƙasar.

Me ya sa ’yan Nijeriya ke ci gaba da shan magungunan gargajiya?

Masana harkokin zamantakewa da lafiya sun ce dogaron da wasu ’yan Nijeriya ke yi ga magungunan gargajiya ya samo asali ne daga abubuwa da dama, ciki har da talauci, rashin wayar da kan jama’a, ƙarancin kulawar lafiya a matakin farko da kuma rashin isasshen tsari da sa ido kan masu sarrafa magungunan gargajiya.

Tsawon shekaru, mutane da dama sun yi imanin cewa gaurayen ganye, saiwoyi da bawon itatuwa na iya magance cututtuka kamar zazzaɓin cizon sauro, typhoid, basir, rashin warfin mazaƙuta, ƙarancin maniyyi da wasu matsalolin lafiya.

Saboda haka, maganin gargajiya ya zama wani ɓangare na rayuwar wasu jama’a, inda ake ganin masu sayar da shi daga tashoshin mota zuwa tituna, har ma da shafukan Instagram da TikTok.

Wasu masu sayar da magungunan suna tallata su a matsayin “ainihin maganin Afirka”, suna kuma iƙirarin cewa sun fi magungunan asibiti ƙarfi.

Sau da yawa ana gaya wa masu saye cewa kofi ɗaya na maganin zai “wanke jikinsu”, amma ba kasafai ake bayyana musu irin sinadaran da ke cikin gaurayen ba, waɗanda za su iya haɗawa da barasa mai yawa, ƙarfe masu nauyi, ɓatattun saiwoyi da wasu sinadarai masu illa.

Talauci na tura wasu zuwa maganin gargajiya:

Mama Halima, mai shekara 47 da ke sayar da ƙosai a yankin Life Camp da ke Abuja, ta ce ta shafe kusan shekaru 20 tana shan “agbo”, kuma rahotannin mutuwar mutane ba su sa ta daina ba.

Ta ce ba ta da isasshen kuɗin zuwa asibiti duk lokacin da ta ji rashin lafiya.

A cewarta, ana iya kashe tsakanin N5,000 zuwa N10,000 wajen samun katin ganin likita, sannan wasu magungunan cutar maleriya na iya kaiwa N14,500.

Sai dai ta ce “agbo” na iya kaiwa tsakanin N200 zuwa N500 kacal, gwargwadon irin cutar da ake son magancewa.

Ta kuma yi imanin cewa ba dukkan masu sayar da magungunan gargajiya ne ke amfani da abubuwan da ba su dace ba wajen sarrafa su ba, tana mai cewa matsalar tana faruwa ne da wasu gaurayen magunguna na bogi.

Ga wasu maza, musamman direbobin motocin haya, amfani da maganin gargajiya ya shafi neman ƙarin kuzarin namiji.

Niyi Adetola, ɗan shekara 38, direban da ke zirga-zirga tsakanin Jabi da Mpape a Abuja, ya ce wasu magungunan asibiti suna sa mutum ya ji rauni, yayin da “agbo” yake ganin yana ba maza ƙarfi.

Shin maganin gargajiya yana maye gurbin maganin asibiti?

Masanin zamantakewa kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a, Aduragba Aminulahi, ya danganta matsalar da talauci, rashin wayar da kan jama’a, ƙarancin tsari da sa ido da kuma raunin tsarin kula da lafiya na matakin farko. A cewarsa, a wasu jihohi, cibiyar kula da lafiya ta matakin farko guda ɗaya na iya kasancewa tana kula da mutane kusan 20,000. Ya ce hakan na sa jama’a da dama komawa wajen masu sayar da “agbo”, har abin ya fara kama da yadda ake zuwa kantin magani.

Ya ce idan babu magunguna a cibiyoyin lafiya, ko ma’aikatan jinya ba sa nan, masu sayar da “agbo” sukan zama wurin da mutane ke iya samu a kowane lokaci. Sai dai wani mazaunin Mpape a Abuja, John Nansal, ya ce har yanzu yana da cikakken imani da tasirin magungunan gargajiya, duk da gargadin masana kan wasu daga cikinsu.

Gwamnati ta bayyana yawan masu fama da cutar ƙoda:

Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta bayyana cewa sama da ’yan Nijeriya miliyan 17 ne ke rayuwa da cutar ƙoda, da yawa daga cikinsu ba su ma san suna ɗauke da cutar ba. Ma’aikatar ta ce amfani da gaurayen magungunan gargajiya na daga cikin abubuwan da za a iya kauce wa da ke haddasa matsalar. Ta kuma yi gargaɗin cewa sakamakon lalacewar ƙoda na iya kai mutum ga buƙatar wanken ƙoda, wanda zama guda a wasu asibitocin gwamnati ke kaiwa kusan N100,000.

Ba mu amince da wani ‘agbo’ a matsayin maganin komai ba – NAFDAC

Darakta-Janar na Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce babu wani gaurayen maganin gargajiya da hukumar ta amince da shi a matsayin maganin cututtuka masu yawa.

Ta ce, abin da ya kashe mutanen Ondo shi ne wani gaurayen tsirrai da ba a tsara yadda ake sarrafa shi ba, ba a auna sinadaransa yadda ya kamata ba, kuma ba a samar da shi cikin tsafta ba, tare da haɗa shi da sinadarin ethanol na masana’antu. Adeyeye ta ce NAFDAC ta fara kwashe gaurayen maganin da ake zargi ya haddasa mutuwar jama’a daga kasuwannin Ondo.

Binciken ɗakin gwaje-gwaje, a cewarta, ya nuna cewa gaurayen ya ƙunshi sinadarin methanol da paracetamol da yawa fiye da ƙa’idar da ta dace. Ta ce an gano ethanol da ya kai sama da kashi 400 bisa ɗari na iyakar da ake ɗauka a matsayin aminci. “Wannan ba magani ba ne; guba ce,” inji ta.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarƙashin Dokar NAFDAC ta shekarar 2023, sayar da gaurayen magungunan gargajiya ba tare da lambar rajista, ranar ƙera shi, adadin da ya kamata a sha da kuma jerin sinadaran da ke cikinsa ba, laifi ne da doka ta haramta. Wanda aka samu da laifin na iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru har biyar a gidan yari.

Likitoci sun yi gargaɗin illar “agbo” ga ƙoda da hanta:

Likitoci sun ce illar da magungunan gargajiya marasa tsari ke haddasawa ba ta tsaya ga waɗanda suka mutu a Ondo ba, domin kullum suna ganin masu fama da matsalolin da suka danganci amfani da irin waɗannan gaurayen magunguna. Dr Olufemi Ogundele, ƙwararren likitan cututtukan ƙoda a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan, ya ce kusan kashi 60 cikin 100 na matsanancin lalacewar koda da ake kula da su a asibitin na da alaƙa da amfani da gaurayen magungunan gargajiya. An kuma bayyana cewa wasu masu sarrafa “agbo” na haɗa tsire-tsiren da ke ƙara fitar fitsari da wasu saiwoyin da ka iya cutar da ƙoda, musamman idan aka yi amfani da su fiye da kima.

Irin wannan haɗin, a cewar masana, na iya haifar da matsalar aiki ko ma durƙushewar koda da hanta cikin ’yan kwanaki. Likita kuma ƙwararren masani kan magunguna, Dr Abubakar Saliu, ya gargaɗi jama’a kan yawan shan magungunan gargajiya, yana mai cewa illolinsu na iya kasancewa ba sa bayyana nan take. Ya ce wasu marasa lafiya kan koma asibiti bayan dogon lokaci suna amfani da magungunan gargajiya, suna fama da ciwon ciki da wasu matsaloli. Ya kuma ce yawan amfani da irin waɗannan gaurayen na iya sauya hawan jini da kuma matakin sukarin jini.

A cewarsa, abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wasu illolin ke bayyana ne bayan lokaci, yayin da mutum ya ci gaba da shan maganin ba tare da sanin cewa yana lalata lafiyarsa ba.

By ukarofi

Leave a Reply