Daga WAKILINMU
Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya tare da haɗin gwaiar Tarayyar Turai da sauran takwarorinsu sun kamala wani shirin yaƙi da cin zarafin mata a Nijeriya mai laƙabin ‘spotlight initiative’ tare da mika ragamar cibiyoyin gudanar da aikin ga gwamnatin Nijeriya.
An kamala shirin ne a otel na Transcorp da ke Abuja a tsakiyar makon nan inda wasu ministoci da shugabannin hukumomin gwamnati suka halarta.
A jawaban da suka gudanar daban-daban, Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mattias Schmale da Wakiliyar Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, Samuela Isopi sun ce shirin ya samu nasara bisa yadda yake bai wa matan da aka ci zarafi damar zuwa cibiyoyin kulawa don sake farfaɗo da rayuwarsu, kana suka ce mika shirin daga gwamnati ne zuwa gwamnati kasancewar su goyon baya suka bayar amma gwamnati ce ta aiwatar da shirin.
Da yake jawabi, Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu wanda Dr. Lare Akanye ya wakilta, ya bayyana cewa, “An samu ci gaba a yaƙi da cin zarafin mata tun daga lokacin da aka ƙaddamar a 2018. Akwai cibiyoyi daban-daban da aka samar a wasu sassa na ƙasa domin gudanar da aikace-aikacen da suka shafi ceto rayukan waɗanda aka ci zarafinsu da kuma sake farfaɗo da rayuwarsu.
“Gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa wurin bayar da goyon baya ga dukkan ire-iren waɗannan shirye-shirye na ci gaban rayuwar ‘yan ƙasa.
Kuma ya yaba wa Tarayyar Turai da ta bayar da kashi 5 cikin 100 na taimakon kuɗin da ta ware a duniya inda Nijeriya take cin gajiyar wajen miliyan 500.” In ji shi
Hakazalika, Ministan Shari’a, Fagbemi Lateef ya bayyana cewa, ya yi magana da ƙungiyar gwamnoni domin fadada tsare-tsare da shirye-shiryen da tarayya ke gabatarwa game da yaki da cin zarafin mata.
Yanzu haka, a cewarsa, ma’aikatarsa ta mike haiƙan wurin ganin ana hukunta duk waɗanda aka kama suna cin zarafin mata, “yanzu haka akwai shirin da muka yi na tabbatar da cewa ana hukunta masu cin zarafin mata a makarantu. Za mu tabbatar da kare ‘yancin waɗanda al’amarin ya rutsa da su da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata sun gurfana a gaban kuliya.
“Muna jin dadin cewa a yau da ake rufe wannan shiri na yaƙi da cin zarafin mata na ‘Spotlight Initiativ’e, an samu ci gaba a kan manufar shirin kuma Wannan ya kara nuna cewa idan muka yi kawance da abokan ci gaba, za mu samar da sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’umma.”
Shi ma a jawabinsa, Sarkin Shonga, Dr. Haliru Yahaya Ndanusa, ya buƙaci al’umma su hada karfi da karfe wajen kawar da dukkan wani nau’i na cin zarafin mata domin kyautata rayuwarsu.
Ya ba da misalin cewa matuƙar aka bari cin zarafin mata ya ci gaba da gudana to babu shakka za a zare musu walwala a rayuwarsu inda hakan kuma zai shafi hatta ci gaban ƙasa saboda mata masu ilimi da ke cikin kwanciyar hankali suna ba da gudunmawa ga ciyar da ƙasa gaba.
