Yadda mata ke sayar da ƙwon haihuwarsu domin sayen abinci a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A faɗin Nijeriya, ana samun ƙaruwar yadda matasa mata ke sayar da ƙwayayen haihuwarsu, domin samun kuɗaɗen biyan buƙatun rayuwa, lamarin da ke haifar da muhawara kan illolinsa ga lafiya da kuma tarbiyya.

Binciken da Weekend Trust ta gudanar ya nuna cewa cibiyoyin kula da matsalolin haihuwa sun zama wuraren da ɗalibai mata da sauran matasa ke zuwa domin sayar da ƙwayayen haihuwarsu. Wasu sun ce sun yi hakan ne domin biyan kuɗin makaranta, wasu kuma domin sayen gashin doki, tufafi da wayoyin hannu, yayin da wasu uwayen da ke renon yara su kaɗai suka ce kuɗin ne ke taimaka musu wajen ciyar da iyalansu.

Abin da a baya ake ɗauka a matsayin taimako ga ma’auratan da ke fama da matsalar haihuwa, yanzu ya koma wata hanya ta neman kuɗi ga mata da dama. Duk da cewa ana biyan masu tsakanin dubban naira zuwa ɗaruruwan dubban naira, masana sun ce aikin yana tattare da haɗurran lafiya kamar Oɓarian Hyperstimulation Syndrome (OHSS), zubar jini da kamuwa da cututtuka, musamman idan ba a bi ƙa’idojin lafiya yadda ya kamata ba.

“Na sayar da ƙwayayen haihuwata domin biyan kuɗin makaranta”

Wata ɗaliba da ta nemi a sakaya sunanta ta ce ta shiga harkar ne bayan wata ƙawarta ta sanar da ita. Ta ce kuɗin makaranta ne ya tilasta mata shiga shirin.

Ta bayyana cewa kafin a amince da mace ta sayar da ƙwayayen haihuwa, ana yi mata gwaje-gwaje kamar tantance rukunin jini, genotype, lafiyar jikinta da kuma duban mahaifa domin tabbatar da cewa tana da isassun ƙwayayen haihuwa.

A cewarta, wasu cibiyoyi sun fi son masu genotype AA, yayin da wasu ke fifita masu rukunin jinin O Positiɓe. Bayan an amince da ita, likitoci kan fara yi mata alluran hormones na tsawon kwanaki 10 zuwa 14 domin ƙara samar da ƙwayayen haihuwa, sannan ana ci gaba da bibiyarta ta hanyar gwaje-gwajen duban dan tayi.

Daga bisani ana yi mata tiyata ƙarama a ƙarƙashin maganin sa barci domin cire ƙwayayen. Ta ce, ta yi aikin sau biyu, inda aka biya ta kusan Naira 300,000 a kowanne karo. Ta bayyana cewa ba ta nadamar matakin da ta ɗauka saboda tana ganin ta taimaka wa mata masu fama da rashin haihuwa.

Hukumar Daidaito da Kare Haƙƙin Mata ta Jihar Filato (PLASGEOC) ta bayyana damuwarta kan yadda matasa mata ke sayar da ƙwayayen haihuwarsu kan kuɗi tsakanin N120,000 zuwa N150,000.

Jami’ar Yaɗa Labarai ta hukumar, Nene Dung, ta ce bincikensu ya gano wata cibiyar haihuwa da ke gudanar da wannan aiki, tana mai bayyana lamarin a matsayin cin zarafin mata da take haƙƙinsu.

Ta ce, wasu daga cikin matasan suna amfani da kuɗin wajen sayen wayoyi masu tsada da gudanar da rayuwa ta alfarma.

Hukumar ta ce, ta fara wayar da kan calibai a Jami’ar Jos, Kwalejin Fasaha ta Barkin Ladi, Kwalejin Ilimi ta Gindiri da Jami’ar Ilimi ta Pankshin domin faɗakar da su kan haɗurran lamarin.

“Ina samun samu N60,000 a kowane karo.”

Wata uwa mai yara uku mai suna Jennifer John (ba sunanta na gaskiya ba), ta ce matsin rayuwa ne ya sa ta sayar da ƙwayayen haihuwarta sau biyu shekaru uku da suka gabata. Ta ce, tana samun N60,000 a kowane karo.

Jennifer ta ce, daga baya wani ma’aikacin jinya ya ba ta shawarar ta shiga aikin ɗaukar ciki wa wasu (Surrogacy), amma ba ta ci gaba da hakan ba. Ta ce, kuɗin da ta samu ya taimaka mata wajen sayen katifa da kula da iyalanta.

Wata ɗaliba mai suna Jumoke Adeyemi ta ce ita da wasu ƙawayenta suna shiga harkar ne domin su ci gaba da tafiya da takwarorinsu. Ta ce, duk da cewa iyayenta na ba ta kuɗi, tana buƙatar ƙarin kuɗin sayen gashin doki, wayoyi da tufafi masu kyau. Ta ce, ta taɓa samun N150,000 bayan sayar da ƙwayayen haihuwarta, kuma ba ta nadamar hakan.

Wasu mata sun bayyana cewa bayan cire ƙwayayen haihuwarsu sun fuskanci matsananciyar rashin lafiya. Wata ta ce, cikinta ya kumbura, ƙafafunta suka yi kumburi har ta yi tunanin za ta mutu.

Daga baya ta gano ta hanyar bincike cewa wataƙila tana fama da OHSS, wata matsala da ke iya biyo bayan amfani da magungunan ƙara samar da ƙwayayen haihuwa. Ta ce, ba a yi mata cikakken bayani kan yiwuwar faruwar wannan matsala ba kafin ta amince da shiga shirin.

Masana a fannin mata da haihuwa sun ce duk da cewa tsarin bayar da ƙwayayen haihuwa yana da aminci idan an gudanar da shi yadda ya kamata, dole ne a tabbatar da cewa an yi wa masu bayarwa cikakken bayani, an ba su shawara kuma ana ci gaba da kula da lafiyarsu bayan an kammala aikin.

Babbar Likitar Mata da Haihuwa, Ali Nafisatu Mohammed, ta ce alluran hormones da ake amfani da su sun daɗe ana amfani da su kuma ana ɗaukarsu a matsayin masu aminci idan an yi amfani da su yadda ya dace.

Shi ma ƙwararren likitan haihuwa, Dr. Akinnagbe Akinbola Fernandez, ya ce yawan buƙatar ƙwayayen haihuwa na ƙaruwa ne saboda mata da dama na jinkirta aure da haihuwa.

Ya ce, ƙa’idojin ƙwararru sun ba da shawarar kada mace ta bayar da ƙwayayen haihuwarta fiye da sau biyu a rayuwarta domin rage yiwuwar matsalolin lafiya. Sai dai ya nuna damuwa cewa Nijeriya ba ta da cikakken tsarin ƙasa da ke bibiyar mata masu bayar da ƙwayayen haihuwa, lamarin da ke ba wasu damar yin hakan a cibiyoyi daban-daban ba tare da an gano ba.

Lauya Redzie D. Jugo ya bayyana cewa Dokar Kiwon Lafiya ta ƙasa ta 2014 (National Health Act 2014) ta amince da bayar da ƙwayoyin halitta domin magani, amma ba ta amince da kasuwancinsu ba. Ya ce, babu wata ƙa’ida ta ƙasa da ke tsara yadda ake ɗaukar masu bayar da ƙwayayen haihuwa, yadda ake ba su shawara, adadin kuɗin da ya kamata a biya su da kuma yadda za a kula da su bayan aikin.

Saboda haka ya buƙaci gwamnati ta samar da cikakkiyar doka domin kare lafiyar mata da kuma daidaita harkokin cibiyoyin kula da haihuwa a ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply