Yadda mata manoma ke kashe kuɗaɗe masu yawa amma ribarsu na raguwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsadar takin zamani da sauran kayan aikin gona na ƙara jefa mata manoma cikin matsin tattalin arziki, duk da shirye-shiryen da gwamnati ke aiwatarwa na rage musu kuɗin sayen kayan aikin noma.

Ga manoma mata da dama a Nijeriya, samun amfanin gona mai yawa a lokacin girbi ba ya ƙara zama tabbacin samun riba. Tsadar takin zamani, magungunan kashe ƙwari, maganin ciyawa da sauran kayan aikin gona ta sa suke kashe kuɗi masu yawa wajen noma, amma daga ƙarshe kuɗin da suke samu bayan sayar da amfanin gonar ba ya wadatar da su wajen biyan kuɗin da suka kashe. A taƙaice, abin ya zama kamar ana ɗaukar kuɗi daga aljihu ɗaya ne domin cike wani, ba tare da an samu wata riba ta zahiri ba.

Matsalar ba ta tsaya ga manoma kaɗai ba, har da mata ’yan kasuwa da ke sayar da kayan abinci da sauran amfanin gona. Su ma suna fama da tsadar sayen kaya da kuɗin sufuri, yayin da suke ƙoƙarin sayar da hajarsu a farashi mai sauƙi ga kwastomomi. Ga waɗannan rukunoni biyu, illar matsalar ta wuce harkokin kasuwancinsu, domin tana shafar kuɗin ciyar da iyali, karatun yara, tanadin kuɗi da kuma zaman lafiyar tattalin arzikin gidajensu.

Alheri Jonathan, wata manomiya da ke Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja, ta shaida wa jaridar Blueprint Weekend irin halin da ta shiga sakamakon kashe kuɗi masu yawa wajen sayen takin zamani da magungunan amfanin gonar masara, amma ta kasa dawo da jarin da ta zuba bayan girbi.

Ta ce, “Na sayi buhun takin zamani a kan naira 54,000, sannan na sayi magungunan da zan yi amfani da su a gonar masarata saboda ina son samun girbi mai kyau. Amma ana sayar da mudun masara a kan naira 450 kacal. Ban ma samu amfanin gona mai yawa ba a wannan kakar, kuma bayan na sayar da abin da na girbe, sai na fahimci cewa kuɗin bai kai wanda zan dawo da jarin da na kashe ba.”

Jonathan ta bayyana halin da ta shiga a matsayin abin sanyaya gwiwa, tana mai cewa duk ƙoƙarin da ta yi a gonar bai haifar mata da ribar da take fata ba.

Wata manomiya, Salamatu Tanko, daga al’ummar Barangoni da ke Bwari a Abuja, ta ce tsadar kayan aikin gona ta sa har ta fara tunanin ko za ta ci gaba da noma ko kuma ta koma wata sana’a. Tanko, wadda ke noman gyada da ƙwan kabewa, ta ce ta nemi rance daga ƙungiyar haɗin gwiwar tattalin arziki da take ciki domin sayen takin zamani a wannan kakar noma.

Ta ce, “A da, ina iya sayen duk abubuwan da nake buƙata a gonata, kuma har yanzu ina da kyakkyawan fata cewa zan samu kuɗin da zan ci riba bayan sayar da amfanin gona. Amma yanzu al’amura sun sauya. Takin zamani da sauran magungunan gona sun yi tsada matuƙa, ta yadda talakawa ba za su iya sayensu cikin sauƙi ba.”

A cewarta, noma na buƙatar kashe kuɗi a matakai daban-daban, tun daga share gona da shirya ƙasa, zuwa kula da amfanin gona da kuma girbi. Sai dai duk waɗannan kashe-kashe ba sa ba manoma tabbacin samun kuɗin da zai wadatar bayan sayar da amfanin gonar.

Matsalar ta shafi matan da ke sana’ar sayar da amfanin gona a kasuwanni. Joy Akpan, wata ’yar kasuwar shinkafa a kasuwar Idah da ke Jihar Kogi, ta koka kan yadda kuɗin sayen kaya da na sufuri ke rage musu ribar da suke samu. Ta ce, “Wani lokaci kwastomomi kan yi ƙorafin cewa farashin kayanmu ya yi tsada, amma ba su san yawan kuɗin da muke kashewa kafin mu kawo kayan kasuwa ba. Bayan biyan kuɗin mota da sauran buƙatu, abin da ya rage mana a matsayin riba ba ya wadatar da buƙatun iyalanmu.”

Wata ’yar kasuwa, Alice Nwankwo, ita ma ta ce tana fama da rashin iya tara kuɗi, saboda mafi yawan kuɗin da take samu daga sana’arta na komawa wajen sake sayen kaya. Ta ce, “Ina aiki kullum, amma ba zan ce ina samun irin ribar da nake buƙata ba. Da zarar na sayar da kayana, sai na yi amfani da kuɗin wajen sake sayen wasu. A ƙarshe, abin da yake ragewa ni da iyalina kaɗan ne.”

Ga mata manoma da ’yan kasuwa, samun rance cikin sauƙi da kuma ƙungiyoyin haɗin gwiwa masu inganci na iya taimaka musu wajen rage matsin tattalin arziki. Sai dai wasu daga cikinsu sun ce tallafin da suke samu ta waɗannan ƙungiyoyi bai kai irin taimakon da suke buƙata ba.

Wata ’yar kasuwa a unguwar Gadu da ke Babban Birnin Tarayya, wadda aka fi sani da Iya Odun, ta ce ƙungiyoyin haɗin gwiwa ba sa samar da tallafin da mata da dama ke buƙata domin bunƙasa sana’o’insu.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirye-shirye daban-daban da nufin rage wa manoma ƙanana nauyin kuɗaɗen noma, tare da inganta damar da suke da ita ta samun kayan aikin gona, rance da kasuwannin sayar da amfanin gonarsu.

A watan Yuli na wannan shekara, gwamnati ta fara rabon buhunan takin zamani sama da miliyan 10 domin tallafa wa manoma ƙanana miliyan biyu a faɗin ƙasar, ƙarƙashin Asusun Tallafa wa ƙananan Manoma da Bunƙasa Amfanin Gona na Renewed Hope. An tsara cewa mata za su kasance kashi ɗaya bisa uku na waɗanda za su amfana da shirin.

Yayin da yake ƙaddamar da shirin, Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ce an tsara shi ne domin magance matsalolin da manoma ke fuskanta tun daga lokacin shuka amfanin gona har zuwa sayar da shi.

By ukarofi

Leave a Reply