Yadda muka kashe sabon shugaban ISWAP – Sojoji

*Su 38 muka halaka a lokaci guda, inji rundunar
*Yayin da 1,199 suka tuba

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Rundunar Sojojin Ƙasa ta Nijeriya ta bayyana cewa, Rundunar Musamman ta Operation Haɗin Kai da ke aikin kawar da ’yan ta’adda a Yankin Arewa Maso Gabas ce ta halaka sabon shugaban Ƙungiyar ISWAP, mai fafutukar yaƙi da kai hare-hare a yankin, wanda aka fi sani da Malam Bako, tare da wasu ’yan ta’addar guda 38.

Rundunar Sojojin ta ƙara da cewa, kimanin ’yan fafutukar da iyalansu 1,199 ne su ka tuba,waɗanda suka haɗa da maza 114, mata 312 da kuma yara 773 a yankuna daban-daban na yankin tsakanin 15 zuwa 28 ga Oktoba, 2021.

Darakta mai Kula da Yaɗa Labarai na Rundunar ta Musamman (DMO), Birgediya Janar Benard Onyeuko, shine ya bayyana haka a jiya Alhamis a Abuja yayin da ya ke sanar da manema labarai ci gaban da aka samu a ɓangaren ayyukan rundunar a faɗin ƙasar ciki har da Wakilin Manhaja a lokacin taron.

Ya ce, “tawagar Operation Haɗin Kai ta ci gaba da yin matsin lamba a Arewa Maso Gabas. Tawagar da aiwatar da hare-hare ta ƙasa da ta sama a gurare daban-daban, lamarin da ya haifar da bai kawai abokan yaqin sun gaza ba ne, a’a, sun ma miƙa wuya ne tare da iyalansu.

“A hakan ne aka gama da kimanin ’yan ta’adda 38, ciki har da jagoransu, Bako. Haka nan, an kama masu tsegumta wa ’yan ta’adda kimanin guda 11 da kuma kayayyakinsu a yayin yunƙurin.”

Bugu da ƙari, ya ce, an kama manyan makamai guda 29 da harsasai 166 da sauran miyagun makamai, yana mai cewa, sauran abubuwan da suka yi sun haɗa da manyan taraktoci guda biyu danƙare da bindigogi da buhunnan taki 622, sannan a ka tserar da fararen hula da suka sace guda biyar.

Ya ce, “wasu daga cikin nasarorin nan an same su ne a ƙauyukan Dar, Kumshe, Wulgo, Chabbol da Kijmatari a Jihar Borno da kuma Ngala – Wulgo da Nguru a hanyar Kano. Sauran guraren sun haxa da ƙauyukan Dikwa da Mafa da ma ƙauyen Ngama a Jihar Yobe.”

Daga nan sai ya ƙara da cewa, saboda yadda ayyukan sojojin ke samun nasara ta ƙasa da sama, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba har kawo ƙarshen dukkan wasu ayyukan ’yan ta’adda a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *