Matarka ka saki ko har ‘ya’yanka?

Daga AMINA YUSUF ALI

Matar ka saka kaɗai ko har da ‘ya’yanta? Na san wannan tambaya ba ni kaɗai ta tsaya wa a rai ba, har ma da sauran ɗimbin masu karatu waɗanda suka kasance mazauna ƙasar Hausa. Ko ma na ce Arewacin Nijeriya. 

Kafin mu shiga bayani gadan-gadan, ya kamata mu sani, shi saki ko rabuwar aure, halastaccen abu ne. Allah (SWT) ne ya ba da dama a aiwatar da shi. Amma duk da haka ya ce, a yi shi cikin mutuntawa. Haka akwai wani hadisi da ya ce, ma fi ƙi a wajen Allah daga cikin abubuwan da ya halatta shi ne saki/ rabuwar aure.

Don haka wanda ya ba da umarnin ma Ya ce yana ƙin sa. Kun ga ko ba abinda hakan yake nunawa sai cewa kada a yi gaggawar saki idan ba da hujjar da ta sa dole sai an yi ba. Ko kuma idan ba a yin ba, akwai matsala.

Idan za mu duba, za mu ga cewa akwai matsalolin da gara a rabun ya fi. Kamar idan ma’aurata suna yawan samun saɓanin da ba ya iya warwaruwa, ko idan mijin ba ya iya sauke ɗaya daga cikin nauye- nauyen da addinin musulunci ya rataya masa na iyalinsa. Ko kuma dai wasu dalilan masu ƙarfi. 

Idan za mu faɗi gaskiya ba goce-goce, a ƙasar Hausa ne aka fi mai da sakin aure kamar cire hula. Wato an fi yin saki barkatai. Amma ba sakin ne abin mamakin ba, yadda uba kan yi watsi da kuma shagulatin ɓangaro da yaransa waɗanda ya rabu da uwarsu.

Tamkar ma tare ya sake su, ko kuma da ma can da su ta zo gidansa aka haɗo mata da su a kayan gara. Abu ma har ya zama ruwan dare gama-duniya. Mutane ma ba su damu ba ana kallo kullum yana faruwa. 

Da farko, wasu mazan da kansu ƙiri-ƙiri  ma za su ce wa mace ta tattara yaranta ta bar musu gidansu. Wannan abin mamaki da yawa yake. Yadda ka san ita kaɗai ta yi yadda za ta yi har ta samar da su. Kobkuma addini ya ce idan ka sake ta shikenan ƙarshen alaƙarka da yaran da kuka haifa.

Abin takaicin ma, idan ta tafi da yaran nan, shikenan gani yake ba ruwansa da kuma nauyinsu da buƙatunsu. Wani ma sai ya shekara nawa bai saka su a ido ba, kuma bai damu ya gansu ]in ba. Shi yana kallo, danginsa suna kallo, al’umma tana kallo za a sakar wa wannan mata akalar rayuwar yaran ta fuskar sha’anin kuɗi da kuma tarbiyya. 

Sauƙi-sauƙin ta ma,  a ce iyayenta suna da hali ko kuma ita tana da wata sana’a mai ƙarfi da za ta ɗauki nauyinsu. Wacce ba ta da shi kuma, sai dai ta koma maula ko ta ta afka wasu muggan hanyoyi don rufa musu asiri. Abinda nake gaya muku kuma shi fa mijin da ya sake ta uban yaran yana can yana rayuwa mai kyau tare da mata ko matar da ya aura cikin wadata. Wataƙila ma fa mai hali ne. 

Wani mijin kuma ba shi zai ce ta tafi da su ba, amma ita ta san ba zai iya riƙewa ba. Wataƙila ma lokacin da suna tare, ita ce ko iyayenta suke ɗawainiya da ita da iyalinta. Ko kuma ta san ba shi da macen da za ta riƙe masa. Ko kuma ta duba ƙanƙantar yaran ta ji tausayinsu, sai ka ga ta kasa haƙura ta bar su. Shi ko gogan naka, da ma rannan kamar Sallah.

An sauke masa dala da gwauron dutse. Sai ya shiga sha’ani ya yi ta fantamawa. Ko ya yi ta aure-auren wasu matan nauyinsa yana ƙaruwa har ma ba ya iya samun rarar kuɗin da zai kai wa tsohuwar matarsa da ‘ya’yansa.

Wata kuma ba za ta bar masa yaran ba, saboda ta san mata ko matansa ba su zauna lafiya tare da ita ba, kuma ba za su riƙe mata yara tsakaninsu da Allah ba. Domin Allah ya kawo mu zamani na cutar da yaran miji da zaluntarsu. Kawai mace idan kishiya ta mutu ko ta fita, shikenan sai ki ɗauki tsanar Duniya ki ɗora wa yaranta. Kin mance ɗa na kowa ne. Idan Allah ya raya su ma, su za su iya ɗaukar nauyinki ma gabaɗaya. Waya san gobe?

Wata kuma, bayan an sake ta, idan ta bar gidan ta dangwarar da ‘ya’yan cikin fushi, ta yi gaba. Sai kuma wani lokacin ta ji mugun labarin da zai dawo da ita, ta tafi da su. 

Idan muka duba dukkan waɗannan dalilai dai za mu ga cewa, tilas ne yake sa uwa ta cigaba da rayuwa da ɗaukar nauyin yaranta bayan an rabu da ubansu. Wannan ba zaɓinta ba ne sam. Amma dai abin dubawar shi ne, yadda ake barin ta da nauyin yaran, bayan ba ta saba ba da haka a rayuwa. Sannan kuma, ba ita Allah ya ɗora wa nauyin ba tun fil’azal.

Laifin waye? 
*Na farko manyan ababen tuhuma su ne hukumomin ƙasar nan. Suna barin maza suna cin karensu babu babbaka. Wasu ƙasashen a Duniya idan ka sake ka rabu da mace, akwai wasu maƙudan kuɗaɗe na ladan gabe da kake biyanta da ake kira da ‘alimony’.

Kai kanka ba za ka fara zancen saki ba ka san kai ne a ruwa. Domin kuɗin zai iya zama fiye da rabin dukiyar da ka mallaka ko fiye da haka. Kun ga ko ai ko wargi ma wuri ya tarar. Kuma kana tare da iyalanka, mace ko yara ka gwada ƙin sake nauyinsu ka ga ikon Allah. Kodayake, a garuruwa kamar Jihar Kano akwai hukumar Hisba amma dai ba ta da ƙarfi sosai. 

Na biyu, Al’umma su ma sun taimaka matuƙa wajen ɗaure gindin maza su yi watsi da iyalansu. An mayar da shi ba wani laifi ba. An fi zagin matar da aka saka da ɗora mata laifi a kan shi wanda bai duba yawan zuriyyar ba, ya koro ta da yara, kuma ya yi wasarere da nauyinsu da ya rataya a wuyansa.

Kuma wannan rashin imanin ba zai sa a hana shi wani auren ba a dai cikin al’ummar. Da a ce ana yin tir da Allah wadai da irin haka, to da wataƙila an samu raguwa. Kuma al’umma idan muka cigaba da goyon bayan irin waɗancan mazan, to lashakka fa su waɗannan yaran idan ba su samu tarbiyya ba, su za su addabe ku, su hana ku sakat da sace-sace da ta’addanci domin an bar su ba abinci, ba tarbiyya. Sannan kuma su za su cakuɗa da naku yaran, su gurɓata musu tarbiyya. Kun ga ba mafita kenan. 

 Na biyu, iyayen matar da mijin  suna ba da gudunmowa sosai. Ya kamata iyayen miji da danginsa duk yadda kuka ƙi wannan matar tasa bayan an rabu ku dinga tunasar da shi haƙƙinsu da yake kanku. Hakan soyayya ce. Domin kuna tunasar da shi ya sauke haƙƙin Allah. Ba so ba ne, kuma ba imani ba ne, ku bar shi ya watsar da yaransa. Don ba su ya saka ba, matar ya saka. Kuma ku ma kun haifa. Idan kuka goyi bayan haka ku ma za a iya gwada wa naku. Haka ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta. 

Haka a ɓangaren dangin mata sai a ɗauki fushi a ƙi a nemi mijin ko iyayensa don ɗaukar nauyin ‘ya’yan. Kuma su iyayen fa ba yi za su yi ba. Kamata ya yi su shige mata gaba, ƙwato mata haƙƙinta har gaban hukuma. Wasu iyayen kuma kunya ce da yakana take musu birki. Ba sa son yin wani abu kada a ce sun yi rashin mutunci. To rashin mutunci kuwa ku aka yi wa ai da aka sako musu ‘ya kuma ka yi watsi da ‘ya’yanta. 

Na uku kuma, matar gidan tana ƙin riƙe yaran kishiya idan ta fita ko ta mutu. Shi kuma tsoron kada ya tilasta ta ta zalunce su, sai ya ba wa uwarsu yaran. ‘Yaruwa ki sani, ke ma ƙaddarar nan ba ta wuce ki ba. Ko ta saki, ko ta mutuwa. Kuma ke ma kin haifa. Sai a ji tsoron Allah, kuma yi a hankali saboda akwai ranar nadama.

Kuma mata don Allah a tsara haihuwa, kuma a nemi sana’a. Ki tsara haihuwarki saboda rashin tabbacin rayuwa irin wannan. Mutumin da kika san zamanki da shi ba mai ɗorewa ba ne, ko ba shi da zuciyar nema da kula da iyali, sai ki taƙaita haihuwa. Haka idan kin san ba ki da sana’a, ki nema. Idan irin haka ta faru, zai fi miki sauƙi a kan a ce sai yanzu ma kike neman san’ar da za ki yi. Haka ɗaukar nauyin zai fi miki sauƙi-sauƙi.

Daga ƙarshe, maza masu waccan aƙida su sani, akwai ranar nadama. Ina yi musu wannan tuni ne, domin  maza da dama ba sa hangen nesa da tunanin akwai  rayuwar gaba. Sukan biye wa jin daɗin yanzu su manta da gaba. Akwai mutuwa, yayana. Za ka je lahira ka girbi abinda ka shuka, khairan ko sharran. Haka akwai hakki. Hakkin waɗancan yara ba zai taɓa ƙyale ka ba. Ba za ka taɓa samun yadda kake so ba a rayuwa matuƙar ka yi watsi da waɗancan yara da ba su ji ba, ba su gani ba. 

Hakazalika, akwai tsufa yana zuwa. Lokacin da ƙarfinka zai ƙare. Masu dabara sukan gina ‘ya’yansu su ba su tarbiyya, su kuma yaran su tallafi tsufan iyayen. Amma sai ka ga iyaye sun yi watsi da yaran an bar su kawai don an saki uwarsu. To Yayana wai uwar ka saka ko kuma har da ‘ya’yan? Su me suka yi? Jininka ne fa, tsatsonka ne fa. Hausawa dai sun ce sai ka yi da kyau, kake ganin da kyau. 

A nan zan dakata, makarantan jaridar Manhaja mai farin jini, ina godiya da fatan alkhairi. Shawarwrinku da yabawa, da tsokaci su suke ƙarfafa ta har kullum. Na gode, mu haɗu a Manhaja ta mako na gaba.