Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ranar Lahadi ne shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana yadda ya yi barazanar korar Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, saboda ayyukan raya kasa a babban birnin tarayya da kuma irin tasirin su na samun nasarar siyasarsa a 2027.
Tinubu, yayin da ya ke magana a lokacin bikin Sallah da Ministan Babban Birnin Tarayya, da manyan jami’an gwamnati suka yi a fadar shugaban ƙasa a Abuja, shugaban ya tuno da tattaunawar da suka yi da Wike a lokacin da ya buƙaci a fitar da Babban Birnin Tarayya Abuja daga Asusun Bai ɗaya na TSA.
Tinubu, wanda ya yaba wa Ministan babban birnin tarayya Abuja kan nasarorin da aka samu a birnin, ya ce “Ya kasance mai gidan kowane babban mutum a birnin.
Tinubu wanda ya bayyana cewa Wike ya sauya tsarin majalisar yankin, kuma ya samu ci gaba maras misaltuwa ta fuskar albarkatu.
“Na tuna ranar da Nyesom Wike ya zo wurina ya ce, ‘Don Allah, ka fitar da mu daga wannan matsalar ta TSA, domin in ƙara yin aiki, kuma na samu nasara.
“Sai na ce, ‘To, gaya min abin da za ku yi.’ Kuma ya gabatar da shi. ‘Shin zai ba ni dama ga jam’iyyata ta lashe zaɓe a Abuja?”
Na ce, “Na san daga ina ka fito, jam’iyyarka ko jam’iyyata, idan wannan abu ya yi yawa a kan ka, za ka rasa aikinka.’ Sai ya ce, ‘To, komai zai yi daidai Oga.”
Kuma abubuwa sun fara canjawa cikin sauri, na fara duba wuraren da aka buɗe karkara, na ayyukan da aka yi watsi da su, kuma gidan mataimakin shugaban ƙasa da aka yi watsi da shi shekaru da yawa ya farfaɗo.
“Ana gyara cibiyoyin kiwon lafiya, ana inganta cibiyoyin kiwon lafiya na mazauna babban birnin tarayya Abuja, ana gyara makarantunmu da gina gine-gine, na gode Wike.”
Shugaban ƙasar a lokacin da yake jawabi tun farko a filin Eid-el-Fitr, Abuja, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su rungumi ɗabi’ar ƙwarai na Eid-el-Fitr ta hanyar nuna matuƙar ƙauna da tausayawa ƙam kan gaskiya, musamman ga marasa galihu, da kuma miƙa ayyukan agaji ga masu ƙaramin ƙarfi.
