Yadda Remi Tinubu ta yaba wa Gwamna Abba ya nuna Kanawa na gamsuwa da ayyukansa – Farfesa Dahiru

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugaban Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha na Jihar Kano (STSB), Farfesa Dahiru Sale Muhammad, ya bayyana cewa yadda Oluremi Tinubu, mai ɗakin shugaban ƙasa, ta yaba wa Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, na nuna gamsuwa da ayyukan da ya yi wa Kano a kowane fanni.

Ya ce yadda ta yaba wa gwamnan tare da karrama shi a lokacin da ta kai ziyara Kano ya ishe su abin farin ciki, godiyar Ubangiji da kuma alfahari, domin wannan ɗaga daraja ce ga al’ummar Kano ba gwamna kaɗai ba, kamar yadda ya bayyana a wannan lokaci.

Haka kuma ya ƙara da cewa akwai buƙatar al’ummar Kano su ci gaba da ba da haɗin kai ga gwamnatin kan ayyukan da take yi a fannin ilimi. Ya ce kowa na gani an sabunta Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kofar Nassarawa da ke kan titin gidan gwamnati, tare da gyare-gyaren sauran makarantun kimiyya da fasaha da sauran makarantu, wanda ya kawo bunƙasar ilimi a Kano.

Ya ce hakan ya bayyana ta hanyar samun kyakkyawan sakamako a jarabawar kammala sakandare ta NECO da kuma jarrabawar ƙualifying, da sauran su, wanda ke nuna yadda ake samun bunƙasar ilimi da sauran fannoni na rayuwar al’umma a Kano.

A ƙarshe, Farfesa ɗahiru Sale Muhammad ya nuna gamsuwa kan yadda gwamnan Kano ya zaɓi matashi Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa, wanda aka rantsar da shi a wannan Talata. Ya kuma buƙaci a ba gwamnati haɗin kai ta hanyar addu’o’i domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki da lafiya a Kano da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi