
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa ya kusa rasa muƙaminsa na Gwamnatin Tarayya saboda goyon bayan da yake ba wa ɗan Majalisar Dokokin Lagos, Desmond Elliot.
Gbajabiamila ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya kira shi yana tambayarsa ko Desmond Elliot mutuminsa ne, bayan zargin cewa yana cikin ‘yan majalisar da suka jagoranci tsige tsohon Kakakin Majalisar Legas, wato Mudashiru Obasa.
Ya bayyana cewa, ya shawarci Elliot da ya fito ya nesanta kansa daga batun tsige Obasa, amma bai yi hakan ba saboda waɗansu dalilai.
Desmond Elliot na wakiltar mazaɓar Surulere, inda Gbajabiamila ya taɓa wakilta kafin ya zama shugaban ma’aikatan.
Rahotanni sun nuna cewa Elliot na fuskantar ƙalubale wajen sake lashe zaɓe yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.
