2027: Tambuwal ya janye tsaya wa takarar sanata yayin da jita-jitar zama mataimakin shugaban ƙasa ta ɗauki ɗumi

Spread the love

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya janye daga batun tsaya wa takarar kujerar sanatn Sakkwato ta Kudu yayin tunkarar zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa Tambuwal, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC kuma na kusa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya ɗauki matakin ne sakamakon sauye-sauyen siyasa da ke gudana a bangaren adawa.

Janyewar tasa na zuwa ne yayin da jam’iyyar ADC a jihar Sokoto ta bayyana sunayen wadanda za su tsaya takara a mukamai daban-daban na zaben shekarar 2027.

Jam’iyyar ta bayyana Alhaji Manir Dan Iya a matsayin dan takarar gwamna, yayin da Ambasa Faruk Malami Yabo zai tsaya takarar Sanatan Sokoto ta Kudu.

Rahotanni sun nuna cewa matakin na ADC na daga cikin shirye-shiryen da jam’iyyar ke yi domin karfafa tsarinta gabanin zabukan fidda gwani da babban zaben shekarar 2027.

By Babaji