Ɗangote ya bayyana dalilin da ya sa ya janye batun sayen ƙungiyar Arsenal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shahararren attajiri a Afirka, Aliko Ɗangote, ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar daina bin burinsa na dogon lokaci na sayen ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, inda ya ce ya fi mayar da hankali kan kammala aikin matatar mai ta Ɗangote.

Ɗangote ya bayyana haka ne a wata hira da shugaban kamfanin Norges Bank Investment Management, Nicolai Tangen, ranar Alhamis.

Ya ce, ya kusa ɗaukar matakin sayen ƙungiyar a lokacin da darajar Arsenal ta kai kusan dala biliyan 2, amma daga bisani ya yanke cewa saka kuɗi a aikin matatar man nasa shi ne abin da ya fiye masa.

Attajirin ya kuma ce ya zaɓi cigaba da goyon bayan ƙungiyar a matsayin mai sha’awa maimakon mallakarta.

“Don haka na yanke shawarar ci gaba da goyon bayansu, ina kallon wasanninsu. Duk lokacin da Arsenal ta buga wasa, ina sanya rigar ƙungiyar. Ni masoyi ne, ya fi kyau na cigaba da kasancewa masoyi kuma na cigaba da zuba jari a kasuwancina”, kamar yadda ya bayyana.

Kazalika, ya ce darajar ƙungiyar ta ƙaru sosai tun daga wancan lokacin, wanda hakan ya sa sayenta ya zama ba mai anfani sosai ba a gare shi.

By Babaji