
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya ƙi amince wa matsin lamba daga magoya baya, abokai da kuma ’yan uwa da suka buƙaci ya tsaya takarar kujerar sanata a babban zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa, ya fi fifita haɗin kan ‘ya’yan jam’iyya akan muradinsa na karan kai na siyasa domin cigaban al’umma da jiharsa.
Gwamnan ya faɗi haka ne yayin jagorantar zaman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Maiduguri gabanin fara zaɓen fidda gwani na masu neman kujera a majalisar wakilai da za a yi ranar Alhamis.
Zulum ya ce, duk da irin kiraye-kirayen da yake samu daga ɓangarori daban-daban, ya yanke shawarar ci gaba da mayar da hankali kan aikinsa na gwamna da hidimar al’umma maimakon shiga takarar siyasa ta Majalisar Dattawa.
Ya ce, a yanzu burinsa shine fifita cigaban jihar Borno da kuma inganta rayuwar al’umma, ba wai neman wani sabon mukami ba.
Haka kuma, ya shawarci jam’iyyar da ta bari a yi zaɓen fidda gwani a wuraren da ‘yan takara suak nuna rashin amince wa yarjejeniyar fitar da ɗan takara.
