2027: Ayala ya fice daga APC zuwa PDP bisa zargin nuna wariya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE

Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Gombe mai wakiltar Billiri ta Gabas, Hon. Rambi Ibrahim Ayala, ya bayyana cewa rashin adalci da nuna wariya ga tsofaffin mambobi ne suka sa ya bar jam’iyyar APC ya koma PDP.

Ayala, wanda yanzu ke neman takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Balanga/Billiri a ƙarƙashin PDP, ya bayyana haka ne bayan kammala tantance shi a sakatariyar jam’iyyar da ke Gombe.

Ya ce tsarin sulhun da APC ta gudanar kwanan nan ya nuna ƙarara cewa jam’iyyar ta fifita sababbin shiga fiye da mutanen da suka daɗe suna aiki domin cigabanta.

A cewarsa, irin yadda aka gudanar da tsarin ya karya masa gwiwa tare da nuna cewa babu daidaito tsakanin mambobin jam’iyyar.

“Abin takaici ne yadda mutum zai kwashe shekaru yana aiki da jam’iyya, amma daga baya a fifita waɗanda suka shigo kwanan nan fiye da shi,” in ji Ayala.

Tsohon shugaban kwamitin shari’a na majalisar dokokin jihar Gombe ya ce siyasar Najeriya ta fi karkata ga anfani da muradu fiye da aƙida, lamarin da ke haddasa yawaitar sauyin sheka tsakanin ‘yan siyasa.

Ya ƙara da cewa ba zai ci gaba da zama a inda, a cewarsa, ba a mutunta ƙoƙarin tsofaffin mambobi ba.

Ayala ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa PDP za ta warware matsalolin cikin gida da take fuskanta kafin babban zaɓen shekarar 2027.

“PDP tana da lokaci da damar sake haɗe kanta kafin zaɓe, kuma ina da yakinin za ta fito da karfi,” ya ce.

Dangane da rade-radin da ke cewa akwai yunƙurin hana shi samun tikitin PDP, Ayala ya ce bai damu da irin waɗannan jita-jita ba.

Ya bayyana cewa a wannan zamani mutane na amfani da kafafen sada zumunta da fasahar AI wajen yaɗa bayanan da ba su da tushe.

“A gare ni, abin da ya fi muhimmanci shi ne na samu nasarar tsallake tantancewa lafiya, kuma ina ci gaba da tuntubar al’umma,” in ji shi.

Ayala ya nuna yaƙinin cewa zai samu cikakken goyon bayan al’ummar mazaɓarsa a zaɓen da ke tafe.

By ukarofi