Da Ɗumi-Ɗumi: Boko Haram ta sace ɗalibai da dama a wata makaranta a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mayaƙan Boko Haram/ISWAP sun yi garkuwa da ɗaliban makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.

Harin ya auku ne a safiyar yau Juma’a a lokacin da ‘yan ta’addar suka kutsa cikin makarantar akan babura ƙasa da mintina 15 da dakarun tsaro suka bar garin.

A wani saƙon Soshiyal Mediya da wani mai suna Mista Solomon Mussa ya wallafa, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce harin ya shafi ɗaliban makarantar ne kaɗai.

Haka nan shi ma mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Abdullahi Askira ya tabbatar wa jaridar Vanguard faruwar harin.

A cewarsa, wasu da dama daga cikin ɗaliban sun tsere zuwa bayan gari yayin da maharan suka yi awon-gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba.

I’zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Borno ba ta fitar da wata sanarwa ba a hukumance akan al’amarin.

By Babaji