JAMB ta sanar da lokacin sauya makaranta da fitar da sakamako

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar shirya Jarrabawar shiga Manyan Makarantu JAMB, ta sanar da fara sauya makarantu da kwas na UTME na 2026 ga ɗaliban da ke buƙatar haka.

JAMB ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafa ta kafar X daga kakakinta, Dakta Fabian Benjamin.

Hukumar ta kuma sanar da cewa za a fara fitar da sakamakon jarrabawar UTME na 2026 na ainihi daga ranar 18 ga watan Mayu, 2026.

Akan haka ne ta shawarci ɗalibai da su ziyarci cibiyoyin CBT da ta amince da su domin ciro takardar sakamakon jarrabawar da suka rubuta da kuma samun damar yin wasu makamantan buƙatu.

Hakan na zuwa ne makonni bayan JAMB ta sanar da sako sakamakon UTME, amma ta jinkirta fitar da takardun sakamakon, saidai ta bayar da damar gani ta saƙonnin kar ta kwana, wato SMS kaɗai.

By Babaji