Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƙasashen Afrika da su ƙara haɗa kai ta fuskar tattalin arziki tare da ɗaukar manufofin da za su bunƙasa masana’antu da ci gaban nahiyar.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron Africa Forward Summit da aka gudanar a cibiyar taro ta Kenyatta da ke Nairobi, ƙasar Kenya, inda ya jagoranci tawagar Nijeriya ta gwamnati, jakadanci da masu zaman kansu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin teku na Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa Afrika, duk da cewa an daɗe ba a yi amfani da shi yadda ya kamata ba sakamakon matsalolin tsaro da rashin tabbas.
Shugaban ya bayyana cewa Nijeriya za ta ƙara haɗa kai da ƙasashen yankin Gulf of Guinea ta hanyar amfani da tsarin Deep Blue Project wajen musayar bayanan tsaron teku domin ƙarfafa tsaro da bunƙasa kasuwanci.
Ya ce tsaro a hanyoyin ruwa, kyakkyawan tsarin doka da haɗin gwiwar ƙasashe su ne za su jawo masu zuba jari da bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Tinubu ya kuma jaddada cewa Afrika ba za ta ci gaba da fitar da albarkatun ƙasa a matsayin ɗanyen kaya tana shigo da kayayyakin da aka sarrafa daga ƙasashen waje ba.
Ya ce duk da shekaru masu yawa da Afrika ta yi da samun ‘yanci, har yanzu nahiyar ba ta kai kashi biyu cikin ɗari na masana’antun duniya ba.
“Afrika na fitar da ɗanyen mai, ma’adanai da kayan gona, sannan tana sake sayen kayayyakin da aka sarrafa a farashi mai tsada. Wannan matsala ta samo asali ne daga tsarin kuɗi na duniya da ke hana ƙasashen Afrika samun jari mai sauƙi domin bunƙasa masana’antu,” in ji Tinubu.
Shugaban ya ce Nijeriya ta ɗauki matakai masu wahala domin gyara tattalin arzikinta, ciki har da cire tallafin mai, haɗa tsarin canjin kuɗi da sake ƙarfafa bankuna da sama da dala biliyan 3.4.
Ya ƙara da cewa duk da waɗannan gyare-gyare, Nijeriya na ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsarin kuɗi na duniya da ke hana bunƙasar masana’antu a Afrika.
Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya za ta kashe kusan dala biliyan 11.6 wajen biyan bashin ƙasa a shekarar 2026, kuɗin da ya ce da an yi amfani da su wajen bunƙasa masana’antu, noma, makamashi da horas da matasa.
Ya tambayi yadda masana’antun Afrika za su iya yin gogayya da na Turai, Asiya ko Arewacin Amurka alhali kuɗin ruwa da ake karɓa a Afrika ya fi nasu ninki biyar zuwa goma.
Tinubu ya ce Nijeriya ba ta neman tallafi ko tausayi, sai dai tsarin kuɗi na duniya da zai bai wa Afrika damar sarrafa albarkatunta, tace ɗanyen mai, ƙera magunguna da yin gogayya a kasuwannin duniya cikin adalci.
Game da batun hijira kuwa, shugaban ya ce samar da ayyukan yi da damar rayuwa a gida ne mafita domin rage yawan mutanen da ke yin haɗarin tafiya ƙasashen waje.
Ya kuma buƙaci ƙasashen duniya su ƙara zuba jari a fannoni kamar sauyin yanayi, makamashi, fasahar zamani da samar da ayyukan yi domin rage matsin tattalin arziki da ke janyo hijira ba bisa ƙa’ida ba.
Taron Africa Forward Summit ya samu halartar shugabanni da jami’ai daga ƙasashe sama da 30, ciki har da shugaban Faransa Emmanuel Macron, shugaban Kenya William Ruto da babban sakataren Majalisar ɗinkin Duniya António Guterres.
