Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da wasu sabbin ka’idoji da suka shafi rantsar da sanatoci da kuma zaɓen shugabannin majalisar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Majalisar ta cimma matsayar ne a zamanta na ranar Litinin, 11 ga Mayu, 2026.
Daga cikin sabbin matakan da aka amince da su akwai cewa duk wani Sanata-zaɓaɓɓe da bai samu damar yin rantsuwar kama aiki da rantsuwar zama ɗan majalisa a ranar farko ta zaman majalisar ba, zai iya yin rantsuwar a duk wani zama na gaba ta hannun Shugaban Majalisar Dattawa.
Majalisar ta kuma bayyana cewa idan Sanata-zaɓaɓɓe ya kasa yin rantsuwa cikin wa’adin da aka tanada, majalisar za ta iya ɗaukar matakin ayyana kujerarsa a matsayin wacce babu mai riƙe da ita tare da sanar da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) domin gudanar da sabon zaɓe a mazabar.
Game da tabbatar da nasarar zaɓe, majalisar ta ce duk Sanata-zaɓaɓɓe dole ne ya gabatar da takardar shaidar nasara da kuma hujjar bayyana kadarori da basussukansa kafin a rantsar da shi.
A sabbin ƙa’idojin da suka shafi zaɓen shugabannin majalisar kuwa, an bayyana cewa Sanata-zaɓaɓɓe na da damar shiga zaɓen Shugaban Majalisar Dattawa da mataimakinsa tun kafin yin rantsuwar kama aiki.
Majalisar ta bayyana cewa za a rika bai wa sanatoci fifiko wajen tsayar da shugabannin majalisa bisa la’akari da yawan wa’adin da suka yi, sannan a bi da tsofaffin ‘yan Majalisar Wakilai kafin sabbin sanatocin da suka fara shiga majalisar.
Haka kuma majalisar ta ce wajen naɗa shugabannin kwamitoci da mambobinsu, dole ne a yi la’akari da wakilcin yankuna shida na ƙasar nan domin kauce wa mamayar wasu yankuna kaɗai.
Majalisar ta ƙara da cewa duk wanda zai tsaya takarar Shugaban Majalisar Dattawa ko mataimakinsa dole ne ya yi aƙalla wa’adi biyu a matsayin Sanata, ciki har da wa’adin ƙarshe kafin zaɓen.
Sannan duk wanda za a naɗa a matsayin babban jami’in majalisar dole ne ya yi aƙalla wa’adi guda ɗaya na shekaru huɗu a majalisar kafin naɗin.
Majalisar ta ce waɗannan matakai za su taimaka wajen tabbatar da tsari, ƙwarewa da daidaito a gudanar da harkokin majalisar dattawa nan gaba.
