Mahara sun kashe mutane biyar, sun yi awon gaba da shanu a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 5 a ranar Litinin a garin Yankamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na dare a lokacin da maharan suka shigo daga jihar Katsina tare da dirar wa ƙauyen.

Mazauna garin sun ce ‘yan bindigar sun yi harbin kan mai uwa dawabi wanda ya jefa al’umma cikin tsoro da kuma mutuwar wasu da dama. Baya ga kashe al’umma, ‘yan bindigar sun sace shanu.

Sunusi Abubakar, shi ne mai garin Yankamaye, kuma ya tabbatar wa da PREMIUM TIMES faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Talata.

Ya kuma yi bayanin cewa akwai wasu da dama da aka harba da bindiga da ayayin da suke ƙoƙarin ɓuya a dazukan da suke kusa da garin.

“Sun zo ne da yamma suna harbe-harbe ta ko’ina,” in ji Abubakar.

“Waɗanda suka gudu daga gidajensu domin neman wurin tsira, sai suka zama abin farmaki na farko. Mutane biyar aka kashe da raunata wasu guda huɗu. An kuma sace shanu daga gidaje daban-daban,” Abubakar ya faɗa.

Basaraken ya ce jami’an tsaron haɗin guiwa da aka jibge a ƙaramar hukumar Tsanyawa sun zo wurin jim kaɗan da faruwar lamarin bayan maharan sun tafi da dabbobin da suka sace ta iyakar Kano da Katsina.

Sani Bala, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ghari/Tsanyawa, ta rubuta a shafinsa na Facebook, ya tabbatar da gane ɗaya daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su. ɗan majalisar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu tare da yi musu addu’a.

ɗan majalisar ya tabbatar da cewa akwai mutane da abin ya shafa kuma suna asibiti suna samun kulawa.

Jihar Kano ta kasance tana da kwanciyar hankali sama da sauran jihohin da suke maƙwabtaka da ita.

Sai dai ƙananan hukumomin Tsanyawa, Bagwai Shanono da Gwarzo sun zama wani sansanin tashin hankali saboda kusancinsu da jihar Katsina wacce ‘yan bindiga suka daɗe suna addabar ta.

By ukarofi