A yau Laraba, tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da sauran waɗanda ake tuhuma tare da shi sun musanta tuhumar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC, ta gabatar musu a gaban Mai Shari’a Maryann Anenih na babbar kotun Abuja. An tuhume su da laifuka 16, amma tsohon gwamnan, wanda shi ne wanda ake tuhuma na farko, ya bayyana rashin amincewarsa da zargin yayin da aka karanta masa tuhume-tuhumen a gaban kotu.
Bayan da aka karanta tuhume-tuhumen, lauyan da ke kare Yahaya Bello, Joseph Daudu SAN, ya gabatar da roƙon beli. Sai dai lauyan EFCC, Kemi Pinheiro SAN, ya ƙi amincewa da roƙon belin, yana mai cewa takardun belin sun daɗe da ƙarewa a watan Oktoba. Amma Daudu ya bayyana cewa akwai wata sabuwar takardar neman beli da aka gabatar a ranar 22 ga watan Nuwamba. Ya ce hakan ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan na mutunta doka tunda ya bayyana a gaban kotu.
A lokacin zaman kotun, EFCC ta bayyana cewa ta shirya fara shari’a nan take tare da gabatar da shaidarta na farko. Amma lauyan Yahaya Bello ya nemi lokaci domin yin shiri, yana mai cewa an miƙa masa takardun tuhume-tuhume da misalin karfe 11 na dare ranar 26 ga watan Nuwamba. Daudu ya yi nuni da cewa wanda ake tuhuma yana da ‘yancin beli domin ya ci gaba da shirinsa na kare kansa a yayin shari’a.
A nata ɓangaren, EFCC ta dage kan cewa wanda ake tuhuma ya yi watsi da wata shari’ar da ke gabansa a kotun tarayya. Sai dai lauyan Yahaya Bello ya ce bai kamata a yi amfani da batutuwan wata kotu wajen hukunta wanda ake tuhuma a kotun Abuja ba. A halin yanzu, sauran waɗanda ake tuhuma tare da shi, Umar Oricha da Abdulsalami Hudu sun sami beli ta hannun EFCC.