Daga UMAR GARBA a Katsina
Ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya NLC reshen Jihar Katsina ta yi barazanar tsunduma yajin aiki sai baba ta gani a faɗin jihar don nuna fushin ta game da rashin fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da ƙungiyar ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya a watannin da suka gabata.
Ƙungiyar ta ce idan har ba ta samu amsa gamsasshiya ba daga gwamnatin jihar a wannan makon da muke ciki, za ta bi umarnin da uwar ƙungiyar ta ƙasa ta bayar a taron da suka yi kwanan nan a Fatakwal na fara yajin aiki a ranar 1 ga watan Disamba, na wannan shekarar a jihohin da basu fara biyan sabon tsarin albashin ba.
Da ya ke zantawa da manema labarai shugaban ƙungiyar NLC reshen Jihar Katsina, Kwamared Hussain Hamisu, ya bayyana damuwarsa kan jinkirin da ake samu a tattaunawa da gwamnatin jihar dangane da biyan sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu babu tabbas game da ƙarin albashi ga waɗanda suka yi ritaya a jihar duk da kwamitin da aka kafa don aiwatar da tsarin albashin ya kammala aikinsa.
“Kwamitin da ke aikin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da gwamnatin jihar ta ƙaddamar ya kammala aikinsa ne bayan cikar wa’adin da aka ɗibar musu.
“Dole ne a yi la’akari da biyan kuɗin waɗanda suka yi ritaya daidai lokacin tattaunawar, duba da cewa akwai yarjejeniya game da haƙƙoƙinsu a lokacin da suka yi ritaya.” Inji shi.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai yi aiki don aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,0000, kwamitin na ɗauke da mutane 15 da za su baiwa gwamnatin jihar shawara kan muhimman dabaru da hanyoyin aiwatar da tsarin.
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Farouk Lawal Jobe ne ya ƙaddamar da kwamitin don samar da dabaru da hanyoyin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi tare da gyare-gyare ga ma’aikata a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Kwamitin wanda sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari ya jagoranta inda aka baiwa kwamitin wa’adin kwanaki 21 ya kammala aikinsa tare da miƙa rahotonsa.
To sai dai kawo yanzu sabon tsarin mafi ƙarancin albashin bai fara aiki ba a jihar.
Dama dai tuni shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa, Joe Ajaero a wani taro da ya gabatar da shugabannin ƙungiyar a Jihar Ribas, ya bayyana cewa duk jihar da ta kasa biyan sabon tsarin albashin, ƙungiyar NLC reshen jihar zata tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.