Gwamna Lawal ya halarci taron AFREXIM a Kenya

Daga USMAN KAROFI

A ranar Litinin, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya halarci taron Africa Sub-Sovereign Network (AfsNET) karo na huɗu da aka gudanar a Kisumu County, Kenya. Taron wanda aka fara daga 25 zuwa 27 ga Nuwamba, ya samu halartar manyan shugabanni daga ƙasashen Afirka, ciki har da Shugaban Kenya, Dr. Williams Ruto, wanda ya buɗe taron a Swiss Grand Royal Hotel.

Gwamna Lawal, wanda ya wakilci Ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), ya kasance ɗaya daga cikin mahalarta wani muhimmin tattaunawa kan samar da mafita mai dorewa ga bunƙasar yankunan Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Sulaiman Bala Idris ya fitar a wata sanarwa.

A jawabin sa, ya jaddada muhimmancin amfani da damar da yarjejeniyar African Continental Free Trade Area (AfCFTA) ke bayarwa domin inganta tattalin arziki da zuba jari.

Ya kawo misalai daga Nijeriya, kamar yadda yankin masana’antar noma na Kaduna ke bunƙasa hada-hadar kasuwanci da kuma yadda yankin kasuwanci ‘yantace na Lekki a Legas ke jan hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje.

“Waɗannan misalan na nuna yadda jihohi za su iya amfani da albarkatun cikin gida don haɓaka tattalin arziki da faɗaɗa kasuwanci,” in ji gwamnan.

Haka zalika, Gwamna Lawal ya bayyana irin rawar da gwamnatocin jihohi ke takawa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa. Ya ce shiyyarsa ta Arewa maso Yamma ta kafa Ƙungiyar Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma domin haɗa kai wajen tsara manufofi masu inganci. Wannan mataki, a cewarsa, ya fara samar da sauyi mai kyau a yankin.

A ɓangaren tsaro, ya yi bayani kan matakan da gwamnatinsa ta ɗauka don tabbatar da zaman lafiya a Zamfara. Ya bayyana cewa kafa rundunar tsaron al’umma, Community Protection Guard (CPG), ya taimaka wajen rage matsalolin tsaro a jihar. Gwamnan ya ce tsaro yana da matuƙar muhimmanci domin samar da kyakkyawan yanayi na ci gaba da bunƙasa tattalin arzikin al’umma.