Yajin aikin jami’o’i: Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya ta caccaki ASUU da Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya wato NANS, ta yi Allah wadai da sabon yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’a ASUU suka sake tafiya.

A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu 2022 ne shugaban ƙungiyar NANS na ƙasa, Asefon Sunday ya fitar da jawabi ga manema labarai, yana kokawa a kan wannan yajin aikin.

Asefon Sunday ya haɗa da Gwamnatin Tarayya da shugabannin ASUU, ya yi masu ta-tas a kan yadda suka gaza shawo kan batun ba tare da rufe jami’o’i ba.

“Mun samu labarin matakin da ƙungiyar ASUU ta ɗauka na shiga yajin aikin jan-kunne na tsawon wata ɗaya tattare da matuƙar takaici.

“Mun yi tunanin ASUU da Gwamnatin Tarayya za su nemi hanyar da za su cinma maslaha, a ɗauki matakin da ya dace na bunƙasa harkar ilmi,” a cewar Asefon Sunday.

Sunday ya ƙara da cewa ƙungiyar ɗaliban za ta shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar nan domin su nuna wa kowa rashin jin daɗinsu.

Ƙungiyar ta ce ba za ta sauka daga matsayar zanga-zanga ba har sai an janye yajin aikin, inda Sunday ya yi kira ga Chris Ngige da wakilan ASUU su koma kan teburin sulhu.

Shugaban ɗaliban ya kuma zargi kowane ɓangare da saɓa doka da rashin yin abin da ya kamata, wanda hakan ya jawo savanin ya kai ga an tafi yajin aikin makonni huɗu.

A cewar Sunday, Gwamnatin Nijeriya da malaman jami’ar sun sa son kai a wajen tattaunawar, ba su yi la’akari da halin da ɗalibai suke ciki ko wanda za su shiga ba.

NANS ta ce gwamnati ba ta yi ƙoƙarin hana ASUU zuwa yajin aiki ba. Sannan ta nemi a riƙa haɗawa da wakilan ɗalibai idan malamai za su gana da gwamnati.

Ƙungiyar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sallami Ministan Ayyuka da na Ilmi, Chris Ngige da Adamu Adamu, bisa zarginsu da rashin shawo kan matsalar buƙatun ƙungiyar malaman jami’o’in.

“Ba za mu tava amincewa ba. Kuma mun yi watsu da shi. Sannan muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggawar sallamar Ministan Ayyuka da na Ilmi. Muna buƙatar shugabanni na ƙwarai, muna buƙatar mutane masu gaskiya,” a cewar sa.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’in (ASUU) ta soma yajin aikin a ranar Litinin ɗin nan don neman cimma buƙatunta a wajen Gwamnatin Tarayya.

Da yake yi wa manema labarai bayani kan matakin da suka ɗauka bayan kammala tattaunawar yini biyu da shugabbanin ƙungiyar suka yi, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce yajin aikin nasu na tsawon wata guda ne a matsayin gargaɗi ga gwamnatin ƙasa.

Ya ce tun a ranar Asabar da ta gabata shugabannin ASUU na ƙasa suka soma zaman tattaunawa a Jami’ar Legas kan batun.

Ya ƙara da cewa kafin soma zaman nasu, sai da suka sanar da malamai da ɗalibai na jami’oin faɗin ƙasar nan game da dalilin da ya sa ASUU za ta tsunduma cikin yajin aiki.

Malaman sun ɗauki matakin shiga yajin aiki ne saboda rashin gaskiyar da suka ce Gwamnatin Tarayya ta nuna musu na ƙin cika musu yarjejeniyar da suka cimma a baya, yarjejeniyar da ta yi sanadiyyar janye yajin aikin da suka yi a 2020.

Farfesa Osodeke ya ce duk da tattaunar da suka yi da Ministan Ƙwadago, Dr. Chris Ngige a Oktoban 2021, kan batutuwan da suka haɗa da farfaɗo da jami’o’in gwamnati, biyan kuɗaɗen alawus, biyan kuɗaɗen ƙarin girma, batun tsarin biyan albashi na IPPIS da sauransu, babu ko guda da aka aiwatar daga jerin buƙatun nasu.

A baya-bayan nan, an ji Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bada tabbacin gwamnatinsa za ta daraja duka yarjejeniyoyin da aka cimma da ASUU don hana aukuwar yawa-yawan shiga yajin aikin a fannin ilimin ƙasar nan.