‘Yan bindiga su kashe mutum ɗaya da sace mutum bakwai a Kaduna

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a unguwar Sabon Gyero da ke Millennium City a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum guda tare da sace wasu bakwai. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga yankin ne da sanyin safiyar ranar Litinin cikin adadi mai yawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da alhini.

Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun nufi wani gida kai tsaye inda suka sace mata uku da ƙananan yara huɗu. Haka kuma, sun kai hari wani wajen cajin waya inda suka harbe wani matashi mai suna Abdullahi Lawal, wanda aka fi sani da “Kurma,” tare da kwashe wayoyi da kwamfutoci daga shagon.

An ce marigayin, wanda kurma ne kuma bebe, ya samu harbi a kai, kuma an garzaya da shi asibiti amma ya rasu kafin isa. Daga bisani an yi masa jana’iza a Sabon Gyero bisa tsarin addinin Musulunci. Wani mazaunin yankin, Adamu Yusuf, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙwazo da riƙon amana, yana mai nuna alhinin rashin da ya yi.

A ɓangaren tsaro kuwa, kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta yankin, Uwaisu Yunusa, ya ce jami’ansu sun tashi bayan jin ƙarar harbe-harbe, amma ba su samu nasarar cafke maharan ba. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Kaduna ko hukumomin tsaro kan lamarin.

By ukarofi