’Yan bindiga sun kashe bakwai da yin garkuwa da dagaci a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin ƙauyen Ƙarfi da ke cikin Ƙaramar Hukumar Takai a Jihar Kano tare da kashe aƙalla mutum bakwai da raunata mutum 3 a yayin harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar ta fara farautar waɗannan ‘yan bindiga.

A ranar Laraba wani ɗan jarida a ƙauyen Sale Hussaini ya ce mahara ɗauke da muggan makamai sun afka ƙauyen da misalin ƙarfe 11 daren Asabar inda suka zarce kai tsaye zuwa gidan Dagaci Abdul-Hayatu Ilu suka waske da shi.

Hussain ya ce ɗaya daga cikin mutum bakwai ɗin da maharan suka kashe makwabcin Abdul-Hayatu Ilu ne kuma maharan sun kashe shi ne saboda ihun da ya rinƙa yi a lokacin da ya gansu.

Ya ce maharan sun kashe mutum biyar a ƙauyen Tudun Makama.

Husaini ya ce mutane bakwai ɗin da maharan suka kashe sun haɗa da Tasi’u Birniyo, Ali Yahaya, Hashimu Amo, Sadiƙu Hussaini, Ahmadu Danlanbu, Bala Audu da Shu’aibu Agwar-maji.

Mutanen da suka ji rauni na asibitin Birnin Kudu dake jihar Jigawa likitoci na duba su.

Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin Arewa da ba ta fama da hare-haren ‘yan bindiga a ƙasar nan. 

Jihohi irin su Katsina, Zamfara, Kaduna ne ke yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga.