‘Yan bindiga sun kashe farar hula 26, sojoji 7 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Aƙalla mutane 26 ne wasu ‘yan bindiga suka kashe tare da wasu sojoji bakwai a ƙauyen Kangon Garacci da ke ƙarƙashin gundumar Ɗangulbi a ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Wani Mazaunin yankin mai suna Malam Bello Ɗangulbi, shi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da Blueprint Manhaja ta yi da shi ta waya a ranar Talata.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 04:00 na yammacin ranar Litinin.

Ya ce, ‘yan bindigar da ke ƙarƙashin ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin da aka fi sani da Ali Kachalla, sun far wa al’ummar yankin da nufin sace musu shanu.

Ya ƙara da cewa, bayan da ‘yan bindigar suka kasa kwashe shanun da suka sace lokacin da al’umma suka fatattake su, sai suka yi wa al’ummar kwanton ɓauna tare da kashe 26 daga cikin su.

Bello ya ci gaba da cewa, ‘yan bindigar sun kai hari kan sojojin da ke da zama a yankin inda suka kashe bakwai daga cikin sojojin.

Ya yi nuni da cewa, mutane da dama sun jikkata sakamakon lamarin, kuma a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Ɗangulbi.

Malam Bello ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su kawo musu ɗauki daga munanan ayyukan ‘yan bindigar da ke addabar yankin.

Blueprint Manhaja ta tattaro cewa harin na zuwa ne a lokacin da Gwamna Dauda Lawal ke tattaunawa da jami’an tsaro kan yadda za a magance matsalar rashin tsaro a jihar a ranar Litinin.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan rahoton, ƙoƙarin samun martani daga rundunar sojin da ke ƙarƙashin Operation Hadarin Daji ya ci tura.