’Yan bindiga sun kashe makiyayi, sun kora shanu 50 a Filato

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga sun kashe makiyayi ɗaya da dabbobi guda 50 da suka haɗa da shanu da tumaki a wani hari da suka kai ranar Talata a yankin Fanzo da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Jihar Fialato.

Alhaji Dan-Azumi, wanda ya rasa shanu 21 a harin, ya faɗa wa Daily Trust cewar, maharan sun ji wa wani makiyayi da ke kiwo a yankin rauni.

Ya bayyana cewa, “Maharan sun faɗo yankin inda suka yi harbi da bindiga. Sun kashe makiya ɗaya sannan sun jikkata mutum ɗaya.

“’Yan bindigar sun yi awon gaba da shanu aƙalla guda 50, wasu daga cikin dabbobin sun mutu, yayin da aka yanka wasu saboda rauni da aka yi musu da alburushi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, Kwamdan Yanki na Huɗu ya kira su taro inda ya buƙaci kada su mayar da martani game da harin tare da ba su tabbacin za a gudanar da bincike kan batun.

A cewar Dan-Azumi: “Mu masu bin doka ne, don haka muna kira ga jami’an tsaron yanki da su gudanar da bincike mai zurfi kan batun sannan a ɗauki mataki kan waɗanda ke da hannu a harin.

“Haka nan, muna kira ga jami’an tsaron da su gano mana dabbobinmu da aka sace.”

By Editor