‘Yan bindiga sun yi garkuwa da gomman yaran firamare a Kaduna

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Jama’a sun shiga halin firgici da  ruɗani  a garin Kuriga da ke  ƙaramar hukuma Chikun a Jihar Kaduna bayan da ‘yan bndiga suka kai hari Makarantar Firamare ta Kuriga (1) da ke yankin inda suka yi awon gaba da gomman yara.

Duk da dai babu tabbaci kan adadin yara da aka sace, sai dai mazauna yankin sun ce yaran za su kai kimanin su 100.

Daily Trust ta kalato cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe na ranar Alhamis.

Wani mazaunin yankin mai suna Shitu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, in da ya ce galibin yaran sun tsare daga azuzuwansu a lokacin da suka ga ‘yan bindigar sun shiga harabar makrantar.

Haka nan, wani ganau, Lawal Kuriga, ya shaida wa Daily Trust maharan sun tattara yaran da suka shiga hannunsu zuwa wani daji.

Ya zuwa haɗa wannan rahoton babu wani tsakaci a hukumance daga ɓangaren gwamnatin jihar.

Kazalika, an kasa samun Kakakin ‘Yan Sandan Jihar, ASP Mansir Hassan balle kuma a ji ta bakinsa kan lamarin.

By Editor