Rashin kiyaye ƙa’idojin rubutu illa ce ga marubuci – Mubarak Jiƙamshi

“Manazarcin Hausa na samun tagomashi mai tsoka a harkar fashin baƙi ko tambihi”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Mubarak Idris Jikamshi, matashin marubuci ne daga Jihar Katsina, duk da kasancewar bai fitar da wasu littattafai masu yawa ba, amma yana da gajerun labarai da dama da ya yi, wasu ma har ya shiga gasannin marubuta da su, a mataki daban-daban. Wani abu da ya bambanta Mubarak da sauran marubuta shi ne kishin da yake da shi a nazarin ilimin harshen Hausa da kula da kiyaye ƙa’idojin rubutu, don yanzu haka yana matakin fara digirinsa na biyu ne a harshen Hausa. Bayan kasancewarsa marubucin labaran hikaya, har wa yau yana nazarin rubutun waƙoƙi da wasan kwaikwayo. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubucin ya bayyana masa irin burin da yake da shi na zama silar samun bunƙasa da ɗaukaka rubuce-rubucen Hausa a duniya bakiɗaya.

MANHAJA: Da farko zan so mu fara da jin cikakken sunanka da kuma sanin ko kai wane ne?

MUBARAK: Cikakken sunana dai shi ne, Mubarak Idris. Amma an fi sanina da Mubarak Idris Jikamshi, musamman a zaurukan sada zumunta. Ni malamin makaranta ne, kuma mai aikin fassara da sarrafa na’urar sadarwa ta zamani, don gudanar da aikace-aikace da suka shafi rubuce-rubuce da zane-zane.

Sannan kuma ina gabatar da wani darasi mai taken ‘Teburin Gyara’ a sahar facebook, domin yin nuni da yadda za mu gyara da kuma bin ƙa’idojin rubutun Hausa.

Ba mu takaitaccen tarihin rayuwarka.

Ni haifaffen garin Jikamshi ne, a Ƙaramar Hukumar Musawa ta Jihar Katsina. Na yi karatun firamare a Jikamshi ‘B’ Primary School daga shekarar 1998 zuwa 2004. Daga nan kuma na shiga makaranar jeka-ka-dawo da ke garin Jikamshi wato, Government Day Pilot Secondary School Jikamshi (GDPSS) daga shekarar 2004 zuwa 2010.

Na halarci Kwalejin Nazarin Ilimin Addinin Musulunci da ke Mararrabar Musawa (CAIS M/MUSAWA) inda na samu shaidar kammala ƙaramar sakandire (BECE) a shekarar 2010.

Na fara karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a Tsangayar Nazarin Ilimin Fasaha (Faculty of Art), sashen Nazarin Harsuna da Al’adun Afrika (Department of African Languages and Culture). Kuma Alhamdulillah, na kammala da sakamako mai daraja ta biyu a (2:1) a shekarar 2015.

Yanzu haka kuma na samu gurbin karatu a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma (Fudma) domin zurfafa karatuna a matakin Digiri na biyu, wato M.A a jami’ar, in sha Allah.

Me ya ja hankalinka ka zavi ka yi nazarin harshen Hausa a matakin jami’a, yayin da wasu ke gudun karatun harshen su na gado?

Alal haƙiƙa tun ina makarantar firamare Hausa ta aure ni. Domin tun daga aji huɗu na firamare har na kammala sakandire, duk malamin da zai zo da littafin zube domin a karanta a aji, ‘yan aji da kansu suke cewa a ba ni, in karanta masu. To, ina jin abin daga nan ya samo asali.

Amma ni a rayuwata na so a ce na karanci darasin lissafi ne (Mathematics), shi ma ba don komai ba, sai don kasancewar lokacin da ina aji ɗaya na ƙaramar sakandire, an yi mana jarabawa na faɗi darasin lissafi. Wannan ne ya sa na ƙuduri aniyar ba zan sake faɗuwa lissafi ba, kuma sai na karance shi in sha Allah. To, ashe ba a nan ƙaddarar tawa take ba.

Tun daga lokacin da na ga sunana a cikin waɗanda suka samu gurbin karatun harshen Hausa a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, sai na ji na gamsu da zaɓin da Allah ya yi mani. Na kuma ɗaura aniyar ganin na yi abin da ya kamata, domin in ba wa mara ɗa kunya.

Na zaɓi in cigaba da karatun Hausa, saɓanin wasu abokan karatunmu da na ji suna ta neman sauya sashen da za su yi karatu. Saboda lura da na yi da irin abubuwan da suke a cikin harshen Hausa, waɗanda suke da muhimmanci sosai.

Na farko dai, duk wanda ya nazarci harshen Hausa matuƙar ya mayar da hankali, to ba lallai sai ya tsaya gwamnati ta ba shi aiki ba, domin yana da jarinsa a hannunsa. Ana yin aikin fassara da tafinta da juya sautin da aka naɗa a rubuce, da tacewasu rubuce-rubucen da wasu suka yi. Duka waɗannan ayyuka ne da sai ka tsadance da mutum kafin ka fara yin su.

Na kuma lura zan iya taimakawa gami da bayar da gudunmawa wurin yaɗawa tare da gyara da kare kyawawan al’adun Bahaushe, domin gudun salwantarsu, idan har ba a nazartarsu a jami’o’i ko makarantu.

Bugu da kari na zaɓi in cigaba da karantar harshen Hausa domin ganin zan taimaki addinina ta hanyar rubutu ko fassara wasu daga cikin littattafan addinin Musulunci. Kuma a ƙarshe haƙata ta cimma ruwa, a dukkan abin da na sa a raina. Alhamdulillah.

Wacce gwagwarmaya ka sha lokacin karatu, kuma yaya sauran abokanka da ƴan’uwa suka kalli zaɓin da ka yi na fagen karatu?

Tirkashi, a gaskiya abin bai zo min da sauƙi ba da fari, musamman kasancewar daga sakandire sai jami’a kawai na tsinci kaina. Amma a gaskiya an ɗan amshi gashi kafin a waye daidai gwargwado. Ban shiga taitayina ba ta fannin nazari, sai da aka manna sakamakon jarrabawa na zangon farko wato ‘First Semester’, lokacin da na ganni na huɗu a cikin jerin mutane mafiya ƙoƙari a ajinmu. Abin ya ɗaure min kai, ya kuma sa na sake nazari da tunani. Wannan abin ya sa na yi azama da sake ɗaura kwarjalle tare da alƙawartawa kaina lallai sai na zamo zakara da yardar Allah. Tun daga lokacin na canza salon karatuna da bincikena. Wanda kuma daga ƙarshe na ga ribar hakan tun a sakamakon da aka fitar a zangon karatu na biyu.

A duka dangina, babu wanda ya tava ɗaga mani yatsa kan zaɓina na karatu. Kowa yana yi mani fatan alheri da kuma bayar da gudunmuwarsa gareni. Sai dai babu wanda ya fi ƙarfafa min gwiwa irin ƙanin mahaifina Malam Musa Nadogo. Shi ne wanda ya riƙa zuga ni, ya sa na ji duk duniya darussa biyu ne kawai ake karanta daga Hausa sai sauran.

Amma daga ɓangaren abokaina kuwa, nan ne na sha fama, domin har a yanzu ɗin nan wasu kallona suke a matsayin wanda bai waye ba, don me zan je in karanci Hausa ina da ƙoƙarina kuma da ƙarancin shekaruna. Sai dai sau tari na kan ba banza ajiyarsu ne, tare da ɗaukarsu a matsayin waɗanda ba su san mene ne rayuwa ba. Ban taɓa mantawa watarana bayan mun fito daga lacca sai abokina yake faɗa min wata magana. “Ka san me ya faru?” Na ce masa, “A’a”. “Wane ne, da ya ganmu mun fito daga aji, sai yake cewa wai wancan ɗan gayen yaron shi ma Hausa yake yi?” Dariya kawai na yi, ban sake komawa ta kan zancen ba.

Waɗanne damarmaki masu nazarin Harshen Hausa suke da shi na samun ayyuka masu tsoka?

Babbar dama mafi girma wadda ba ta da alaqa da aikin gwamnati ita ce aikin fassara da tafinta da kuma juya sauti zuwa rubutu. Domin gaskiya idan Allah ya sa ka haɗu da wani aikin na juya sauti ko fassara ko kuma tafinta to Malam shi kenan fa kai kakarka ta yanke saƙa. Kuma waɗannan wasu ayyuka ne waɗanda dole sai an yi su, sai dai ya danganta da hanyar mutum.

Har ila yau manazarcin Hausa na samun tagomashi mai tsoka a harkar fashin baƙi ko tambihi a harkokin da suka shafi harshe da al’adu ko adabi. Bugu da qari manazarcin harshen Hausa na da damar yin aiki a gidajen jaridu da na rediyo ko talabijin, sannan uwa-uba aikin koyarwa. Da dai sauransu.

Ba mu labarin yadda aka yi ka samu kanka cikin sha’awar rubuce-rubucen Hausa?

Masu iya magana dai na cewa kowanne marubuci daga makaranci ya soma. Haƙiƙa yawan karance-karancena da kuma kallon finafinai su suka ja ra’ayina na tsunduma harkar rubutu. Domin labarina na farko da na fara rubutawa a shekarar 2010 ya samo asali ne daga kallon wani fim ɗin Hausa da na yi. A ranar ban iya barci ba, sai da na feqe alķalamina na sa ɗambar fara rubuta labarina.

Daga bisani kuma, harkar gasa, musamman gasar gajerun labarai ita ce kanwa uwar gamin tsundumata cikin harkar rubutu ka’in-da-na’in, duk da dai za a iya cewa faɗuwa ce ta zo daidai da zama.

Ita kuwa fannin waƙa, yawan karanta waƙoƙin abokaina marubuta waƙa a sahar Facebook su ne suka yi min jagora wurin ganin na fara rubuta tawa waƙar, kasancewar galibin duk wanda zai rubuta waƙa to, in sha Allah idan zan yi sharhi, ni ma zan yi ne a waƙe. To, daga nan ne ni ma na fara rubuta waƙoƙi.

Fannin wasan kwaikwayo kuwa, gaskiya a jami’a na fi yin nazarin wasannin kwaikwayo akan na zube. Wannan ne ya sa na samu sha’awa, amma sai dai duka-duka guda ɗaya kaɗai na iya rubutawa, shi ma na rubuta shi ne ga ɗaliban makarantar sakandiren al’umma ta garin Jikamshi (Community Secondary School Jikamshi), daga shi kuma ban sake rubuta wani ba.

Banda a makaranta wane ne ya tallafa maka wajen fahimtar ƙa’idojin rubutu da fahimtar dabarun rubutu?

Idan har aka ce ban da a makaranta to, gaskiya mutum ɗaya ne. Shi ne Baba Farfesa Ibrahim Malumfashi. Ya yi ɗawainiya da ni sosai dangane da yadda zan tsara labari da kuma lura da dabarun rubutu.

Littattafai nawa ka rubuta kawo yanzu?

Ban da wancan tsohon littafin da na rubuta mai suna ‘Ƙaddara’ wanda shi ma ba a buga shi ba. Ban taɓa buga littafi sukutum ba. Sai dai a yanzu haka, ina da shirin tattara labaraina aƙalla guda 10 ko 12 domin in fitar da su a littafi guda.

Ka taɓa shiga gasar gajerun labarai ne, da sauran marubuta ke shiga, irin na ƙungiyoyi da kafafen watsa labarai?

E, gaskiya na shisshiga gasanni da dama, kuma har yanzu ina kan shiga, domin ko yanzu na ji an saka gasa to, in sha Allah zan shiga.

Gasar farko da na fara shiga ita ce ta Gasar Gajerun Labarai da jaridar Aminiya-Trust ta shirya a 2020, mai taken ‘Dambarwar Siyasa’, inda na shiga da labarina mai suna “Dambarwar Siyasa”.

Daga nan ba sake jin ɗuriyar wata gasa ba, sai a gasar rubuta gajerun labarai da HIBAF ta sanya. Kodayake su tasu gasar wanda ya samu nasara ne zai karɓi tukwicin bita kan dabarun yadda ake rubuta gajerun labarai, ba wata awalaja aka saka ba. Cikin nasara na rubuta labarina mai suna ‘Kai Dai Ka Ga Mutum,’ a shekarar 2021, wanda kuma karansa ya kai tsaiko, aka kira mu bita. Daga ƙarshe kuma aka sa muka sake rubuta labarai, inda na rubuta labarina mai suna ‘Dakarun Canji’ wanda labarin ya samu gurbi a mataki na biyar, kuma aka buga a cikin littafin ‘Furen Ķarya’ da aka wallafa a shekarar 2023, aka kuma gabatar da shi a taron HIBAF 2023.

Sannan na sake shiga gasar gajerun labarai ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa ta 2021, da labarina mai suna ‘Gidan Haya’, sai dai bai kai labari ba. A 2022 ma na sake shiga gasar da labarina mai suna ‘Da-Na-Sani,’ wanda shi ma bai kai bantensa ba.

Bayan nan sai na samu labarin Gasar Dr Umar Radda Sabon Shafi a 2023. Ita ma dai ban yi ƙasa a gwiwa ba, na shiga da labarina mai suna ‘Wanda Bai Ji Bari Ba,’ wanda aka wallafa shi a littafi mai suna ‘Mizani’ a shekarar 2023. Akwai kuma wani labarina mai suna ‘A Dare ɗaya’ wanda shi kuma jaridar Aminiya ta wallafa shi a ranar Jumma’a 7/4/2023 a shafi na 30.

Menene yake baka sha’awa a harkar rubuce-rubucen adabi da rayuwar marubuta?

Babu abin da ya fi burge ni a rayuwar marubuta illa irin yadda suke ɗaukar junansu tamkar tsintsiya, babu wata nuna wariya ko kyama. Suna mutuntawa da karrama junansu. Sannan manyan marubuta suna ƙoƙari sosai wajen ganin sun dafawa na ƙasa masu tasowa da shawarwari da ma wasu abubuwan waɗanda ba shawarwari ba. Zumuncin marubuta shi ma yana daga cikin abubuwan da suke ba ni sha’awa matuqa.

Dangane da rubuce-rubuce kuwa, babu abin da ya fi ban ķaye irin yadda zan ga ana wasa da harshe, ma’ana amfani da salon sarrafa harshe a cikin rubuce-rubuce. Gaskiya duk rubutun da babu salo a cikinsa ni bai fiye burgeni ba. Amma idan salonka ya kama ni, to kuwa fa ba ni ganin littafinka ko littafinki in tsallake. Domin masana na cewa, salo shi ne yake sayar da adabi, wato duk rubutun da babu salo, za ka ji shi lami, ba daɗi.

Haka nan yawan taruka na ƙarawa juna sani da kuma ƙaddamar da wasu littattafan marubuta lallai su ma suna ba ni sha’awa sosai.

Yaya ka ke kallon cigaban harkar rubutun adabi a Jihar Katsina?

Gaskiya ina iya cewa da zuwan siyasar 2023, adabi ya samu uwa da uba har ma da kaka a Jihar Katsina. Domin a cikin shekaru biyu kacal sai da aka gabatar da gasar gajerun labarai daki-daki har guda uku, waɗanda kuma dukkansu manyan ‘yan siyasa ne suka ɗauki nauyin gabatar da gasar ba don komai ba, sai don cigaban adabi, da kuma neman al’umma. Wannan ne ya ƙara tabbatar mana da cewa, ashe adabi wata hanya ce ta tallata duk wata haja da mutum yake ɗauke da ita.

A gaskiya a wancan lokacin sai sambarka! Amma tun da aka kammala zaɓe, ya zuwa yanzu shekara guda, ba a sake saka wata gasa ta rubutu ba a siyasance.

Mu marubuta na Jihar Katsina kam gaskiya mun godewa Allah, domin adabi yana samun tagomashi sosai ta fannoni daban-daban. Idan muka ɗauki ƙungiyar Marubuta ta Jihar Katsina (KMK) irin hovvasar da take yi, don ganin cigaban adabi a Jihar Katsina, lallai sai mu ce sambarka.

Ko wata guda ba a yi ba, ƙungiyar ta shirya wata Gasar Muhawara a bukin murnar ƙarin shekara na ƙungiyar, wanda a gasar na samu na yi na ɗaya. Kuma suka ba ni kyautar littattafai waɗanda ban tava tunanin samunsu ko mallakarsu ba.

Bugu da ƙari, na samu labarin Jami’ar Tarayya ta FUDMA tana shirin wallafa waƙoƙin wani ɗan ƙungiyar KMK wato Maluman Matazu, wanda yanzu haka ana kan tantance waƙoƙin. Ka ga wannan ma aikin cigaban adabi ne.

Sai dai duk da haka, a nan ba zan yi ƙasa a gwiwa ba, zan yi kira ga mahukunta da su taimaka wurin ganin an samar da littattafan koyo da koyarwa na zamani na harshen Hausa, maimakon littattafan labarai. Su ma littattafan tatsuniya da na wasannin gargajiya musamman na wannan zamani gaskiya sun yi ƙaranci kuma akwai buqatar a samar da su, ko don harkar koyo da koyarwa.

Wanne ƙalubale matasan marubuta ke fuskanta a duniyar rubutun Hausa?

Babban ƙalubale ko tarnaƙin da ya dabaibaye matasa masu tasowa ke fuskanta a duniyar rubutun Hausa ba ta wuce rashin jarin wallafa littattafan da suke rubutawa ba.

Ƙalubale na biyu, shi ne yadda mafiya yawan matasanmu na yanzu, ba sa son yin karatu kowanne iri, matukar ba na makaranta ba ne da za su don cin jarabawa. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka tsole mana idanu kuma suka dusasar da hasken rubutu da marubuta da yawa, har ma ya zama barazanar sauyawar ayyukan wasu marubuta.

Akwai kuma babban ƙalubale na wasu daga cikin ɓoyayyun marubuta, waɗanda suke ɓoye kawunansu, suna yin rubutun batsa. Wanda hakan yake jefa da yawa daga cikin zaƙaƙuran matasan marubuta cikin damuwa da tsangwama, kasancewar duk ana yi mana kuxin goro ne.

Da wannan nake son al’umma su sani, da yawan marubutan batsa, ba za su iya fitowa su bayyana kansu a matsayin marubutan batsa, ko su riƙa saka sunayansu na yanka a jikin labaransu ba. Don haka a riƙa yi wa marubuta adalci, mu ma ba jin daɗin abin da suke yi muke ba, ba mu da yadda muka iya ne.

A matsayinka na wanda ya nazarci harshen Hausa, shin kana ganin marubuta na yanzu suna ba da gudunmawa wajen samar da littattafan ilimi na koyarwa ko na tatsuniyoyin yara?

Sosai kuwa, gudunmuwar marubuta ga harshen Hausa wajen haɓakawa da samar da littattafai wani abu ne wanda yake a bayyane. Domin galibi ko marubuci bai kai littafi yawo ba a duniya. Kuma muna ganin yadda rubuce-rubucensu ke yawo a cikin manya da ƙananan makarantunmu na ƙasa.

Sai dai da yawan marubutan mun kawar da kanmu daga rubuce-rubucen ilimi da suka shafi littattafan koyo da koyarwa da kuma na tatsuniyoyi waɗanda za su dace da manhajar ilimi ta ƙasa.

Da wannan nake kira ga ‘yan’uwana marubuta da mu ba wa mara ɗa kunya, wurin ƙarfafa wannan fanni, domin ganin shi ma mun inganta shi, kamar yadda muka inganta fannin littattafai na labarai. Na tabbata za mu iya.

Wanne fagen rubutu ka ke ganin za ka fi ba da gudunmawarka, in ka samu dama?

Gaskiya zan fi bayar da gwaggwaɓar gudunmawata ne ga fannin samar da littattafan koyo da koyarwa na harshen Hausa, musamman na firamare da sakandire. Kasancewar wannan fanni ne da yanzu muke da ƙarancin abubuwan karantawa musamman a makarantun firamare da sakandire, yawancin littafan sun tsufa ba a jaddada su, ko sake buga su ba.

Bayan rubutun zube, shin kana rubutun waƙoƙin Hausa, ko wasan kwaikwayo?

E, nakan taɓa rubutun waƙoƙi, kamar yadda na yi bayani a baya, sai dai ban cika yin su kamar rubutun zube ba. Hasali ma da farko rubutun waƙa gaskiya yana ba ni matuƙar wahala, amma dai yanzu kam Alhamdulillah na samo bakin zaren. A yanzu haka ina da waƙoƙi guda biyar, waɗanda na rubuta a sahar facebook. Wacce zan iya tuna sunanta ita ce ‘Sana’a Sa’a.’

Ta fannin wasan kwaikwayo kuma kamar yadda na faɗa a baya, guda ɗaya tal na tava rubutawa, shi ma an gabatar da shi ne a makarantar al’umma ta garin Jikamshi (Community Secondary school Jikamshi) a shekarar 2019.

Matasan marubuta da dama na komawa rubutun fim ko wanda zai kawo musu kuɗi masu yawa, kai ma kana kan wannan layin ne?

E, gaskiya ne, da yawan matasan marubuta sun faɗa harkar rubutun finafinai gadan-gadan, saboda babu wanda zai ƙi hanyar samu. Musamman idan muka lura da bayanin da na yi a baya, yadda da yawan makaranta labarai yanzu sun cirewa kansu sha’awar karatu, maimakon haka sun raja’a ga kallace-kallacen finafinai. Ka ga kuwa dole idan rawa ta canza kiɗa ma sai ya canza.

Amma daga ɓanagarena, a yanzu kam ba na ciki kuma ban tava kawo zan fara rubutun fim ba a nan kusa. Amma ina ji a jikina watarana ni ma in sha Allah, zan shiga cikin marubuta labaran fim domin a dama da ni.

Idan ka samu dama wanne abu za ka yi ka kawo canji a yadda marubuta ke tafiyar da harkokinsu?

Idan har Allah ya ara min wannan damar. Abu na farko da zan fi mayar da hankali a kai shi ne bayar da bitar yadda marubuta za su inganta rubutunsu ta hanyar kiyaye ƙa’idojin rubutu, da kuma kiyaye al’adunmu na gargajiya. Domin idan ba a lura da ƙa’idojin rubutu ba, to ma’anar takan karkace a rasa ina marubucin ya fuskanta.

Zan kuma ƙarfafawa ķananu da manyan ƙungiyoyin marubuta ta yadda za a kula da rubututtukan marubuta, tare da inganta su, da kuma samar da hanyar da za a riqa wallafa su a sauƙaƙe.

Zan kuma tallafa musamman ta hanyar samar da littatafan tarihin Hausawa da kuma na wasu al’adunsu da na manhajar ilimi ta ƙasa waɗanda su ma gaskiya ba mu cika kai alƙalaminmu fannin ba.

Sannan zan sanya kwamiti mai ƙarfi wurin lura da magance waccan babbar matsala ta masu rubutun batsa, duk da a adabance ba laifi ba ne, amma ya savawa al’adar Bahaushe. Kuma zan shige gaba wurin ganin wannan fanni na rubutun batsa na yi masa kwaskwarima ta yadda zai dace da zamani da kuma al’ada.

Wacce ƙungiyar marubuta ka ke, kuma wanne abubuwan cigaba ka ke amfana da su a ƙungiyar?

Ni mamba ne a ƙungiyar Marubutan Jihar Katsina (KMK), wato ita wannan ƙungiyar zan iya ce maka ba ta da ta biyu a wurin ganin an ciyar da adabi da al’adu na al’ummar Bahaushe gaba.

A cikin wannan ƙungiya ina ƙaruwa da yadda suke sanya bita da kuma gasar gajerun labarai ta hanyar bayar da qwaryar-ƙwaryar awalaja duk don a ƙarfafawa marubuta gwiwa.

Kasancewar mutum a cikin ƙungiyar da zauren gudanar da shirye-shirye na qungiyar kaɗai zai sa mutum ya fa’idantu da abubuwa da yawa, musamman yadda masana adabi suke bitar yadda ake shirya labarai da kuma waƙoƙi.

Wanne buri ka ke da shi a rayuwarka wanda nan gaba ka ke so ka cimma?

Rai da buri in ji ɗiyan Bawo. Ina da tarin buruka a rayuwata mabambanta. Sai dai babbansu gabaɗaya, shi ne fatan in gama da iyayena lafiya, in mutu ina Musulmi mai cikakken imani.

Ta ɓangaren rayuwa kam ba su ƙirguwa, sai dai a ɗan tsakuro. Babban burin da na tasa a gabana yanzu shi ne ganin na kammala muhallina da na fara, domin an ce muhalli sutura, in kuma samu wadda za ta riƙa gadin wannan muhallin daidai gwargwado.

A fannin rubutu kuwa, ina da burin in zama ƙaƙuza in yi tambari a duniya kamar yadda Abubakar Imam sunanshi ya karaɗe nahiyar Afirka a fannin rubuce-rubuce.

Ko da Allah bai nufa zan zama zakaran-gwajin-dafin marubuta ba, ina fatan ya zamana da hannuna ko tunanina a wajen samar da wanda zai taka zuwa sama a havakar rubutu.

Ta yaya ka ke gani za a kawo cigaba a harkar rubutu, kamar yadda ake gani a harkar fim?

Za a iya samar da ci gaba a harkar rubuce-rubuce matuƙar hukuma ta shiga kuma ta yi dumu-dumu da damuwar marubuta da inganta rubutu, kamar yadda ta yi a harkar fina-finai. Domin duk wani ɗan fim da bazarmu, mu marubuta yake rawa, idan har babu marubuci to, babu fim, babu ‘yan fim, babu furodusa babu darakta babu duk wani abu da ya danganci fim da shirya shi.

Abu na biyu shi ne a ƙarfafa Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i kamar yadda ake da ita a Jihar Kano a samar da ita a ko’ina, kuma a ba ta ƙarfi wurin ganin an inganta rubuce-rubucen Hausa. Domin da yawan mutane sun rage karance-karancen labarai ne saboda rashin tsabtace rubuce-rubucenmu. Na tabbata idan muka yi haka, za mu ƙara ciyar da harkar rubutu gaba fiye da yadda ake gani a harkar finafinai.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?

Akwai karin magana da yawa waɗanda suke tasiri a rayuwata, amma karin maganar nan da ake cewa ‘Ka ji, ka ƙi ji, ka gani, ka ƙi gani,’ ita ce wadda ta fi yin tasiri a ilahirin rayuwata. Sau tari nakan buga hujja da ita a wajen bayar da misali a harkokin rayuwata daban-daban.

Na gode.

Alhamdulillahi. Ni ma ina godiya.