‘Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara

Rahotanni daga jihohin Zamfara da Kebbi sun ce ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 40 a ƙauyukan jihohin yayin harin da suka kai da asubahin ranar Lahadi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar, wasu ‘yan sanda guda shida na daga cikin mutum 36 da ‘yan bindigar suka kashe a Ɗan Umaru da ke yankin Zuru a Jihar Kebbi.

Mazauna yankin sun ce an yi jana’izar mutum 27, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harin.

Kazalika, sun ce ‘yan bindigar sun sace mutane da dama haɗi da shanun jama’a yayin harin da suka kai ƙauyuka maƙwafta.

Bayanai sun ce maharan sun kashe mutum uku a ƙauyen Shinkafi, Jihar Zamfara.

Ya zuwa haɗa wannan labarin hukumomin ‘yan sandan jihohin da lamarin ya shafa ba su ce komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *