‘Yan bindiga sun kashe Shugaban Miyetti-Allah a Kwara

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu ƴan bindiga sun harbe Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti-Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Abubakar Idris Sakaina.

A ranar Asabar da misalin ƙarfe 10 na dare ne lamarin ya auku, a ƙofar gidansa dake Oke Ose a Ilorin.

Wani shaida ya ce, makasan nasa ba su karɓi komai daga gare shi ba, inda bayan sun harbe shi, nan take suka yi tafiyar su.

Mai taimaka wa gwamnan jihar kan Alaƙar Yankuna, Muhammad Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga ƴan jarida a safiyar ranar Lahadi.

Ya ce, tuni ƴan sanda suka fara gudanar da bincike game da kisan jagoran al’ummar Fulanin.

Marigayin mai shekaru 32 tsohon mai taimaka wa ciyaman ɗin ƙaramar hukumar Moro ne kuma shugaban matasan Fulani na Kwara.