Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Aƙalla ‘yan bijilanti 70 ne aka ruwaito sun mutu a wani rikici da ‘yan bindiga da ya faru a kusa da ƙauyukan Kukawa da Bunyun da ke ƙaramar Hukumar Kanam, Jihar Filato.
Manhaja ta rawaito cewa mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Litinin, lokacin da daruruwan ‘yan bijilanti daga ƙaramar hukumar Wase ke kan hanyarsu ta zuwa maboyar ‘yan bindiga, amma sai aka yi musu kwanton ɓauna kuma aka kashe da dama daga cikinsu.
Shugaban ƙungiyar ‘yan bijilanti na Kukawa, Aliyu Baffa, ya shaida wa wakilin Manhaja cewa “fiye da ’yan bijilanti 70 aka kashe” a harin na kwanton ɓauna, yana mai cewa akwai yiwuwar a sake gano ƙarin gawarwaki a cikin jeji.
A cewar Baffa, harin ya auku ne kusan kilo mita ɗaya daga garin Kukawa, lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa ‘yan bijilanti kwanton ɓauna yayin da su ke hanyarsu zuwa wata maɓoya da ke cikin gandun dajin gwamnati da ake kira Madam Forest, wanda ke iyaka da wasu al’ummomin jihohin Bauchi da Taraba.
