‘Yan bindiga sun kashe ‘yan siyasa 5 a Inugu

Daga WAKILINMU

A ƙalla mutum biyar ake fargabar sun mutu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai wa wata mota ƙirar Sienna mallakar ɗan takarar sanata na Jam’iyyar a shiyyar Inugu ta Gabas, wato Barista Oyibo Chukwu.

Majiyarmu ta ce harin ya auku ne ranar Laraba a yankin Amechi Awkunanaw da ke cikin Ƙaramar Hukumar Inugu ta Kudu a jihar.

Wani ganau ya ce maharan sun banka wa motar wuta ne alhali akwai mutane a cikinta.

Bayanai sun nuna waɗanda lamarin ya shafa suna kan zagayen tallata ɗan takararsu ne inda suka gamu da ajalin nasu.

Sai dai babu cikakken bayani kan ko harin ya ritsa da ɗan takarar.

A hannu guda, wasu fusatattun matasa a yankin sun kai wa motar ɗan takarar majalisar wakilai na ƙasa na Jam’iyyar PDP a shiyyar Inugu ta Arewa/Kudu, Hon. Ofor Chukwuegbo.

Jaridar News Point ta rawaito cewa direban motar ya riga mu gidan gaskiya sakamakon ƙona motar da maharan suka yi.

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu cikakken bayani ko direban ne kaɗai a motar sa’ilin da aka kai harin.

Kazalika, ya zuwa haɗa wannan rahoto babu wani bayani a hukumance daga ɓangaren ‘yan sanda kan batun.