‘Yan bindiga sun sace tsohon babban Manajan NPA a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Wasu gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun sace tsohon Janar manajan hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA Bashir M. Abdullahi.

Rahotanni sun ce, ɓata garin sun sace shi ne a wata gonarsa da ke garin Sitti da ke yankin ƙaramar hukumar Sumaila da yammacin ranar Laraba da ta gabata,

To sai dai kuma rahotanni sun ruwaito cewa, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ba ta samu rahoton sace shi ba,

Wasu mazauna garin da lamarin ya faru ne dai suka shaida wa manema labarai faruwar lamarin.

A cewarsu da alama ɓata garin sun jima suna fako sa gabanin su ɗauke shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *