Daga Oxford Zuwa Maiduguri: Labarin Farfesa William Richards

Daga PORTIA ROELOFS

Marubuciyar wannan ƙasida wata Baturiya ce mai suna Portia Roelofs, wacce ɗaliba ce a Kwalejin St. Annes College da ke Jamiar Oxford, mai gudanar da bincike kan harkokin siyasa da mulki a Afrika. Ta rubuta ƙasidar ne kan wani shehin malamin jamia a Jamiar Maiduguri, Farfesa William Richards, wanda ya rasu shekaru biyu zuwa uku da suka gabata. Ga yadda ƙasidar ta kasance:

Danshin ɗumin iskar bazara na shekara ta 2019 ya daki fuskata. A tsaye na ke ƙiƙam a ɗakin saman benen gidanmu. A lokacin, ba abunda ƙwayoyin idanuwana suke yi illa ba wa cikinsu abinci ta kallon sanyayyar sararin samaniyar birnin Landan a safiyar wannan  ranar. A nesa da ni, doguwar tukurwar eriyar gurin da ake kira da Alexander Palace ce tsaye a gaba na, kamar mai ɗaga min hannu. A nan ne aka fara haskawa da yaɗa hoto mai motsi mara hatsa-hatsa, a duka faɗin Duniya a cikin shekarar 1936. Ƙiirrr! Na ji amon wayar salulata ya daki dodon kunnuwana, sai kuma sautin murya ya fito daga goshin wayar tawa; sai na tsinci sautin muryar kamar na radiyon da mai ita ke ƙoƙarin sai ta tashar da yake son kamowa. ‘FARFESA,’ shi ne sunan da ya bayyana a kan fuskar wayar salular tawa, ɓaro-ɓaro.

Wannan ita ce haɗuwarmu ta farko da Shehin Malamin a fagen ilimin dabbobi, wato ‘Zoology’ a Turance. Ya kira ni ne domin ƙarƙarewa a kan shirye-shiryen tafiyata ta ƙolonta a cikin watan na Satumba. Hakan ya faru ne biyo bayan biɗar da Farfesan ya yi ga tsohuwar jamiar da ya kwankwaɗi iliminsa daga gare ta, da ta aiko ɗalibi ko  ɗaya domin yin ƙolanta na tsawon wata guda a jami’ar da ya shafe sama da shekaru 15 yana koyarwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wannan wayar tamu ta farko da shi, sai ta sosa min inda yake min ƙaiƙayi, a maɓuɓɓugar tunanina dake gaban ƙwaƙwalwata wajen fara rubuta wannan taaziyyar tasa tun kafin ya rasu. Da zarar na ji kan alƙalamina ya fara alamun dakushewa, sai na yi sauri na wasa shi. Haka na zamanto ina kai gwauro, ina kai mari domin ganin na kammala rubuta taaziyyar tasa wacce ke tsakankanin yan yatsunka a yanzu.
Ba wasu maganganu muka yi ba a wannan yammacin. Ya yi tunanin zan zo ne a watan Yuli mai kamawa, amma sai aka samu jinkirin fitowar bizata har sai da watan Agusta ya kama. Ban samu damar kammala shirye-shiryen zuwan nawa Gabas ɗin ba sai bayan wata ɗaya da yin wayar tamu. Da na bijiro masa da wanne irin ƙarin shirye-shirye zan yi domin jin daɗin zaman nawa a Maidugurin, sai na ga ya basar da tambayar tawa. Kawai ya shiga zayyano abubuwan da ya kamata na kiyaye, da kuma abubuwan da ya kamata na yi guzurin su kamar haka:

“Kina da buƙatar yin guzurin maganin  rigakafi ga zazzaɓin cizon sauron nan mai naci da ke marabtar mutum tun daga ranar farko. Kada ki yi shiga wacce ba ta mutunci ba, ki tabbatar da ƙwaurinki da idon sawayenki a rufe suke! Kullum, kada ki rabu da yan canji a jikinki domin tsaro ba don tsoro ba. Saisaye gashin jikinki kaɗan zai rage miki jin zafin da ake yi a  can.

Bayan sati biyu da yin wayarmu, sai muka haɗu ido da ido. Da na je wajen da za mu haɗun, sai aka yi min jagora zuwa ga wani gini irin na ƙasaitar nan, kai ka ce a masarautar Zazzau kake saboda ƙayatuwarsa. Sunan wajen Farmers Club dake wajen wani gini da ake kira da Whitehall. Daga nan, sai na gangara ta wata farfajiya da aka caɓa wa ado da irin duwatsun nan na ƙasaita masu ɗaukar idanu da sanya nutsuwa ga zuciyar mai kallo. Sai na tsinci kaina a wani ɗaki da wani dogon teburin sa wa a ofis. Sila-silan zarurruakn haske sun cika ɗakin abun gwanin shaawa! Sai gani na suka kai ga siffar mutum ya hakimce a kan kujera a can ƙarshen dogon teburin dake a ɗakin.

Sai surar Farfesan ta ringa bayyana a gare ni kamar yadda hasken rana ke dawowa bayan kisfewarta da kan bayu ga samun dare-biyu. Sai gashi zaune a kan kujerar tasa tarwai. Sai na ji muryar tasa a lokacin kamar ta lokacin da muka yi waya. Kawai dai idanuwansa ne na gan su ba can can shuɗaye ba da Bature ke kira da blue eyes. Sai kuma na ga gashin girarsa sun tanƙwara sun yi lif-lif abunsu. Da alama an ba su kulawa; abun gwanin ban shaawa.

Alummar Tibi asalin su sun shigo Najeriya ne daga ƙasar Kwango, sai Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da su a matsayin yan doka (yan sanda) da sojoji a lokacin. Sun yi hakan ne saboda halin ba sani-ba-sabo da Tivin ke nunawa yayin aikin nasu a cikin alumma. Hakan ya faru ne, saboda ba su da dangin iya bare na baba a ƙasar , a wancan lokacin. Babban abunda ke riƙe aure a cikin ƙabilar Dinka ta Kudancin Sudan shi ne aladarsu ta biyan sadaki da manyan-manyan shanu ga dangin amarya, duk lokacin da auren ya mutu, to fa wajibi ne iyayenta ko danginta su yi kashinsu.

Yana ajiye wannan zaren labarin na Dinka, sai ya fara saƙa wani labarin, amma a wannan lokacin abubuwan da muka tattauna a waya akasari su ya ƙara labarta min. A wannan ɗakin da nake zaune da aka ƙawata da ledar kwalliyar bango mai tambarin fulawowi, daga baya kuma muka rankaya wani ɗakin cin abinci, wato dining room dake kallon bishiyoyin lambun da ake kira da Victoria Gardens da kuma ɗaya lambun da ake kira da Thames dake a baya. Tun daga wannan rana, rayuwarmu ta ɗauki wani salo ni da shi da ya haifar da alkhairai da yawa. Sai na zamanto tamkar ɗalibi a gaban malaminsa dake shiftar duk abunda ya fito daga bakinsa. Wasa farin girki!

Bishiyar Koko, wato yayanta, wanda mu muke kira da Cocoa suna da ɗabi’ar adana iskar Nitrogen a cikinsu. Duk yayin da ta sauka a kansu. Daɗin daɗawa, ga daɗi a baki, ga shi cike suke da sinadarin Protein da yawa a cikin su. A yankunan da suke da wadatarsu, ba sa yi wa mazauna wajen wahalar samu su sha ko su yi amfani da su. Har ila yau, za ki iya yin launukan abinci daban daban da su. Kawai dai ƙamfar samun ruwan ne matsalar. Ga ƙoshi ga kwanan yunwa kenan! Shin mafitar hakan na zuwa ne daga masana Ilimin noma da kiwo? Ko kuma sai dai alumma su daki ta kabari su ƙaurace wa muhallan nasu? Faɗin ƙasa ba matsala ba ne. Kowa na iya zama a duk inda yake son zama ya wataya. Masu hikima na cewa ilimi shi ne gishirin rayuwa. Ina mamakin yadda alummar wannan yankin ba sa cancana ruwan saman da suke samu na tsawon watanni uku zuwa huɗu ta hanyar adana shi a dam-dam na ruwa da suke da su da sauran gwalalo. Akwai abubuwan koya da yawa daga Turawan mulkin mallaka.

Yana kai aya, sai kuma ya kamo wani zaren labarin ya fara ƙulla shi. A wannan saƙar bayanin ne ya zayyano min sunayen nauikan saurayen da suke da su a Maiduguri da kuma guraren da ake samun kowanne nauin nasu. Lange-lange mai ramar ƙeta! Sai kuma ya gangaro bayanin ƙabilun Najeriya da yankunan da ake samun kowannensu. Hausa/Fulani ne rabin yawan alummar ƙasar. Sai kuma Yarabawa da Inyamurai da ke biye mu su. Sai na ga ya ranƙwafa kai ka ce Mallam Zurƙe ne lokacin da yake zana jinjirin wata a turɓaya. Ya zana min taswirar gurin da za mu yi haɗuwarmu ta biyu, wato Maiduguri.

Lokacin da Turawan mulkin mallaka suka zo Maiduguri, babu bishiyoyi da yawa a garin. Yawancin bishiyoyin dake a garin, kawo su aka yi. Amma su jamian kula da ƙara girman filin ƙasa ta noma na lokacin babu abunda ke gabansu banda yadda za su samu sahalewar hukuma wajen yin harkokin su gabagaɗi. Saboda a lokacin, iya girman filin noman da ka shata, iya shagalinka.

Bayan mun gama cin abincin dare, sai muka fito domin mu samar masa  tasi ya hau, ta kai shi gida. Har yanzu Farfesa bai daina zuba jawabi ba; kamar dai abun wasan yara da aka wana shi bai gama hucewa ba. Da muka ƙosa da jiran taksi ɗin da har yanzu ba ta zo ba, sai muka gangara ƙasa muka ji yaya tsarin otal ɗin kusa da mu yake. 

Barka da dare, Ya furta yayin da ya ƙaraso gare mu kai-tsaye. Sai kuma muka ga ya zura hannu cikin rigarsa, wato jacket kamar mai ɗauko wani abu. Da ya juyo gare ni, sai na ga ya miƙo min ɗan ƙaramin kundinsa na adana bayanai da kuma wayar salularsa.

Kira Anita, za ki ga sunanta cikin ɗan kundin nan nawa. Farfesan ya biɗa. Lambobin wayar dake cikin kundin nasa ba wasu masu yawa ba ne, ba su wuce 4 zuwa 5 ba bakiɗayan su, kowacce lamba tsarin rubutun sharƙiyyar da aka yi amfani da shi wajen rubutata daban ne da na yaruwarta. Ko dai ka ga tsurar sunan mutum kawai, ko kuma sunan otal a ƙasan lambobin. Na ringa dubawa har na lalubo lambar da aka sa Anita, na kira na miƙa wa Farfesa, ya kira yana jira, ƙarar runjin shigar wayar ba irin na wayoyi samfurin Chana ba ne. Sai na gusa daga gare shi na ƙarasa filin Trafalgar Square, mai cike da haske; na tsaya Ina jiran na ga Ina kuma za mu dosa daga nan.

Tafiyar awa bakwai ce a mota daga filin jirigin saman Mallam Aminu Kano dake Jahar Kano zuwa garin Maiduguri. Sule Buba Sara, wani tsohon ɗalibin Farfesa ne sama da shekaru ashirin, wanda a yanzu tsahon shaƙuwar su ya sa sun zama abokan juna. Lokacin da na sauka, shi ne ya zo ya tarbe ni bayan na sauka daga mota a Maidugurin. Ga mu nan, ga mu nan, mu ne muka keta ta Jigawa, Bauchi, Yobe, sai ga mu a Borno. Sai na tarar da ƙasar waɗannan garuruwan ja-ja-ja-ja, yaluwa-yaluwa, mai kama da jan lemon zaƙi. A kan hanyar mu ta zuwa gidan Farfesan, Na ga abubuwan kallo gwanin shaawa, ido mai na ci ban baka ba? Baki na saki galala ina kallon wata rayuwa da alumma ba irin tawa ba. Ban gushe ba Ina kai gwauro, ina kai mari tsakanin kundin adana bayanaina da kuma tsinin alƙalamina. Duk abunda na gani, sai da na rubuta shi, na zayyana shi; kamar daga hasumiyar masallaci da take can sama da ta tuna min da tukurwar (eriya) gidajen talabijin. Can kuma a ɓarayin (gefen) titi masu sayar da fetur ne da ake kira da yan cuwa-cuwa ke cin karansu ba babbaka. Wani lokacin kuma, Idan na waiwaya geffaina, sai na ga Fulani masu kora shanu. Su ka]a wancan, su shawo kan wancan, su ma suna cin kasuwar ƙasarsu. Haka dai ƙwayoyin idanuwana suka ringa sagaraftu suna ba wa cikinsu abincin da ba su taɓa ɗanɗana irinsa ba, bare kuma ya isa ga tumbinsu.

Emiritus ne sunan da aka raɗa wa Farfesa suna da shi a gidan Sule.  Da fatan dai biro da takardarki ba su yi nisa da ke ba ko? domin da sauran bayanan da ba ki ji su ba. Aiki ga mai ƙare ka! 

A yayin ne ya bayyana min yadda ya taimaka wajen gina Jamiar da ake kira da ‘Free University of Libya; kafin daga baya dole ta sa ya bar ƙasar  saboda hayaƙin da Shugaba Muhammad Gaddafi ya yi masa. Da ya kai zaren wannan labarin ga marinsa bayan ya ɗauko shi daga gwauronsa, sai kuma ya koma kan gwauron wani labarin daban a kan rayuwarsa a Jamiar Oxford tun yana da jajayen sawaye. Hakan ya ba ni damar sanin abubuwan da ban sani ba dangane da ƙuruciyar tasa ta karatu a wannan Jamiar ta biyu a nahiyar Turai sama da shekaru 700 da suka shuɗe. Da ya idar da wannan zaren labarin, sai kuma ya fara kamo zaren rayuwarsa a lokacin yaƙin Civilian Defence Force. Har labarin wata ƙara da ta razana kowa a Oxford University wata rana da daddare a gaban gidan mutan da na Jamiar da ake kira da University Museum sai da ya labarta min. Da aka ƙarasa gurin da aka ji runjin ƙarar, sai aka ga ashe wani namijin bushiya ne da matarsa mayen giyar soyayya ya buge su, suke faranta wa junansu, haɗe suke da juna kamar kifin kantu. Zarurrukan labaran da yake ta saƙawa, sai na gano ba iya wanda ya saƙa da kansa ba ne kaɗai, har da sauran alummar da ya yi rayuwa tare da su. Maana, ba iya kaɗai rayuwarsa yake faɗa ba a lokacin, kamar dai jakar magori ce mai ƙunshe da abubuwa da yawa. Labarin da har yanzu na kasa mai wa ga saƙa zarurrukan labarin bare kuma na kai ga fahimtarsa shi ne, wanda ya ce wata rana ya hau jirgin ƙasa daga Cape Town zuwa Johannesburg a ƙasar Afurka Ta Kudu, wane tudu wane gangare, sai kawai ya tsinci kansa yana ta rausaya rawa da wata mace wacce a ƙarshe dai har ta gamsu da cewa shi ba ya daga cikin Turawa fararen fata masu nuna wariyar launin fata.

Ya ba ni labaran ne yawancisu yayin da yake shan iska a barandar gidansa dake a cikin Jamiar wanda a ka fi sani UNIMAID. Zaune a kan kujerarsa mai kama da karaga, daga shi sai gajeren wandonsa. Duk yayin da aka ɗauke wuta yayin da  muke tsaka da zaman namu, da wahala ka iya hango shi a duhun. Haka nake zama a gabansa kamar a makarantar soro, ina sauraron sa. Nakan jiƙe sharkaf da gumi saboda zafin garin. A gefe guda kuma Sule da boyi-boyinsa mai suna Momo suna ta zuƙulƙular Indomie haɗe da shan kofi (gahwa) Duk lokaci irin wannan, sai na ji kamar burujina ne kacokan ya narke a cikin nasa yake kuma jujjuya shi yadda ya so kamar dai alƙalami a hannun marubuci. Sai na wayi gari na ji kamar mun jima tare da shi, wataƙila saboda tsananin shaƙuwa, wataƙila kuma sanadiyyar wani abu daban. 

Na taɓa hawa katafaren hamshaƙin jirgin ruwan ne na ƙasar Ingila da ake wa laƙabi da P+O Cruise lokacin da na je can ƙasan ƙasar Kanada. Kana tsaye a kansa kana kallon teku iya ganin ka za ka ringa ganin halittar nan ta ruwa mai gashi buzu-buzu da ake kira da Sea otters(dagen ruwan teku) suna yawatawa da shaƙatawa a kan ɓudagen gunguman dusar ƙanƙara abunsu, abun gwanin ban shaawa. “Ƙaramin tiren abinci kake so ko babba?” Ake tambayata Idan mun zo cin abincin dare. Duk wanda ya gan ni a zaune a yayin ya san ba wasa a tattare da ni. Na so na farauto ɗaya daga cikin dagen ruwan tekun nan da suke kai wa da komawa abunsu a cikin ruwa. Kar ka ga yadda yawunsa ya tsinke yayin da ya gano a Najeriya nake aiki. Amma sai na ƙi ba shi kai bori ya hau. Sai na gwammace duk wanda ya ƙyalla ido ya gan ni ko muka haɗa ido da shi, ya san daga inda na fito – wato farin Bature mai kan Banasare ne daga Ingila. Ban cika ɗaukar kururuta abunda yake a ɓoye ba a matsayin cimma buri, sai dai a lokacin ma a ka fara.

A yayin da na fara zama yar gida a Najeriya, sai na fara jin naɗar bayanan Farfesa sun fara zama kayan gabas a kaina.

Dole na zama mai takatsantsan daga waɗanda za su iya kawo min farmaki don kwantar da shaƙuwar shaawarsu a kaina. Haka kuma, dole ne ki zama mai sanya idanu  a kan makusantanki da za su iya ɓarar miki da garinki, kuma ba lallai su tsince miki dukka ba. Kuma kada ki sake ki ba da kai bori ya hau ta yadda mutane za su gane rauninki, don hakan ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba. Nakan ɗan taɓa taya ɓera, ɓari a wasu lokutan, amma hakan ba ya kai wa ga shafar zamantakewata da iyalina. 

Ina nufin, zamanki a nan garin da du-du-du ba ki wuce makwanni uku ba, na san za ki iya danne ƙawazucin sha’awe-sha’awen da ke bijirowa mace a wasu lokutan.

Na gano Farfesa na da yawan magana a ɗan zaman da na yi da shi a lokacin. Ko kuma ka ce ma ya saba da magana. Aa, wani ma ya yi rawa bare ɗan makaɗi?
Yaran Mallam Sule, wanda mu ba lallai a yankin mu na Turai za a iya kiran su da kalmar yaran ba, koyaushe ƙoƙarin zulle wa zama su ka]ai da Farfesan za ka ga suna yi. Saboda idan ya fara zuba kamar ruwan sama yake; tsayawar sa sai ya isa ga aya ba waƙafi ba. Rumfarsa wato falonsa, wacce ba wani isasshen haske ne da ita ba ko da kuwa da rana ne, a saman garunta akwai hotonsa kafe cancaras da shi a lokacin da kansa babu ko ɗison silin furfura, sawayensa kuma lokacin dukansu jajaye ne jawur da su gwanin shaawa. Idan ka sake Farfesa ya dama furar hirarrakinsa da kai, to kuwa dole ku shanye ta tare, ko da kuwa ta yi daɗi ko kuma ta yi akasin hakan. 

Wasu lokutan, ni ma da nake baƙuwa, idan ya yanka min kazar hirarrakin nasa, dole sai na fige ta, ko da kuwa na bayar da uzurin jikina babu da]i, duka domin dai na gudu na huta a ɗakina. Hannuna a ƙage a kan doron farar takarda ta, yan yatsuna guda uku na farko a riƙe da alƙalamin rubutuna, wuyana a sage don jimawa wajen kallon Farfesan yayin da yake ƙulla wancan zaren labarin, idan tufkar tasa ta kusa suncewa, sai ya riƙo shi, Idan kuma ya kufce masa, sai ya kamo wani zaren labarin daban. Amma fa duk suncewar da zarurrukan labaran nasa za su yi ba ya sanya Farfesan ƙin bin sawun su ya kamo su ya tufke su tsam waje guda. A sha ruwa a koma aiki!

Ina mamakin yadda  Najeriya ke wasa da damarta wajen samun kuɗaɗen shiga daga masu yawon buɗe ido, wato tourism. Waɗanda za su ɗauki jinkar kula da hakan ba su fi a ƙirga ba daga cikin yawan alummarta kusan miliyan ɗari biyu. Hakan ba ƙaramin ƙayi da janyo hankalin masu yawon buɗe ido zai yi ba. Ƙasar cike take da abubuwan alada da zamantakewar alumma da ba za su ƙirgu ba, bare kuma a iyakance su. Kin ga dai a yankin Kudancin ƙasar suna da wasan dodorido da ake kira da masquerade masks. A Arewa kuma ga irin su Bikin Kamun Kifi na Arugungu da ake yi a Jihar Kebbi, wanda a da ake kira da Kogin Sokkoto. A nan Maiduguri kuma ana Hawan Daba da dawakai.

Daɗin daɗawa, na gano ba dukkanin maganganunsa da na naɗa ba ne sababbi ko kuma farkon jin su. Akasari, ana samun maimaice, ko kuma kwan-gaba, kwan-baya na maimaita abubuwan da ya riga ya faɗa min a baya. Daga tattaunawar mu da shi ta waya da kuma zaman da muka yi da shi a Farmers Club za ka gane hakan. Idan yanayin gari ya yi zafi, ko kuma abubuwan da muka tsara a kan gudanar da binciken namu ba su tafi yadda muka so ba; ko a ka samu jinkiri; ko makamancin hakan, sai ka ga Shehin Malamin naka ya fara ƙosawa ko nuna alamun gajiya. Da na saka maganganun nasa da na naɗa Ina sauraro, sai na ji ashe wasu maganganun ma ba iya maimaici ba ne, face wasu zantuka ne da suke sarƙewa ko cakuɗuwa da junansu.

Wasu lokutan kuma, sai Shehin Malamin ya kasa wawuro zaren labarin nasa da yake tufkawa, ko kuma Idan ya fara saƙa zarurrukan labaran nasa sai su cukurkuɗe masa, ko kuma ya yi ta saƙa iri ɗaya da zare ɗaya ba tare da ya sani ko ya kula ba. Da Ina bitar shiftar da na ɗauka yayin da nake yi masa tambayoyi a kan rayuwarsa yana ba ni amsa, ga abunda na rubuta a wani shafi kamar haka: 

Kina kuwa tare da ni? Daidai kuwa nake faɗa. Ya faɗa muryarsa a ƙasa. 
Idan idanuwanki suka bar kaina sai ki mayar da su kan Sule. Hakan ya yi kyau. Ya faɗa, yayin da yake kaɗa kansa. 

Ba ni aron kunnuwanki na gaya miki wata magana ta hikima. Ki zamanto mai ganin abubuwan yadda suke a haƙiƙarsu, ba yadda ki ke son ganinsu ba. 

Can kuma, sai barci ya ɗauke shi. Tsarabar Maiduguri da na taho da ita Birnin Landan ba ta alawa ba ce ko kayan ƙwalam da maƙulashe ba, a’a, tsarabar litattafan da na cika da shiftar da na ɗauka ne daga Farfesa. Kai har ma da takardu da su ma na yi rubuce-rubuce a cikin su na lankafe su, wasu ba za ka ce a cikin haske na rubuta su ba, saboda yadda zubin rubutun yake. 

Duk shekara, Idan ya zo Landan hutun shekara muna haɗuwa a wajen da muke haɗuwa wato Farmers Club domin ɗara bibiya da yin karatu na biyu da na uku a kan labarurrukan da ya ba ni a kan rayuwarsa da nake aiki a kan su. Zaman namu kai ka ce kamar muhti ne da alƙali – duk abunda ya faɗa, zan rubuta kamar dai mai yi min shifta. Duk da dai akasarin zantukan da suke gangarowa daga ƙwaƙwalwarsa su fito ta bakinsa ko dai ka ji su bayanai ne a kan imani ko aƙida ta addini, ko kuma waɗansu kalmomi da ake yawan furtawa don samun nutsuwar zuciya ko makamancin hakan. wasu kuma waƙoƙi ne ko zantukan da aka lazimci yin su, ko dai wasu abubuwan masu kama da hakan. Idan da a ce kafatanin tattaunawarmu da shi rubutun allo ne, da sai na ce ban san adadin sau nawa na wanke allon nawa ba. Na kunna hirar tamu a rediyo na ji tare da sauraron ta sannan na dawo da ita kan takarda ban san adadi ba. Kafatanin hirarrakin namu sun dawwama a cikin kundin nawa tsakankanin shekarun 2009, da 2011, da 2012, da kuma 2013 asin da asin ba tare da baddala harafi ko wasali ba. Duk lokacin da na zo ƙara sabunta hirar tamu da Farfesan, sai na ji kamar Ina kekkewayawa ne a wani abu mai kama da keken ɓera.

Ma’ana, sai na ji kamar Ina ta juyawa ne a waje ɗaya. Sai na wayi gari kamar wacce ta narke kacokan a cikin zarurrukan labaran nasa. Wato sai na zama labarurrukan nasa, su ma suka zama ni. Ko kuma na aro kalmar malamin nan Sigmund Freud da ya kira hakan da ‘introjection’. 

Ɗan’adam yana shuɗewa a tsakankanin zamanunnuka guda biyu: Zamanin da ɗan adam ɗin ne ke cikinsa kuma yake sarrafa shi yadda ya so, da kuma zamanin da zamanin ne ke cikin ɗan adam ɗin, ta yadda a lokacin shi mutum ba shi da kataɓus a kan sarrafa zamanin. Waɗannan misalan guda biyu na kwatanta rayuwar Duniya ne da kuma ta lahira bayan an mutu. Amma abunda ya fi kowannensu muhimmanci shi ne, yaryaɗa iri na abunda zai kawo sauyi ga alumma, da kuma shuka bishiyoyin da za su yi yaɗo su cika duniya da ƙanshin furanninsu.
 
Ana rubuta taaziya ko marsiyyar farko da alƙalamin marigayin kafin ya rasu, maana alƙalamin da ya zana rayuwarsa kuma ya gudanar da ita. Daga nan kuma, sai alƙaluman masoya da abokan arziki su yi ta kaikawo a kan fararen takardu masu santsi. Ina ma a ce Ina da isassun tubalan ginin kalmomin buɗe wannan rubutun taaziyyar tawa ga Farfesa; da na buɗe rubutun taaziyyar tawa kamar haka: 

A ranar Laraba ta watan Febrairu a shekarar 1920 a ka samu  a gidan Styan Richard, a rukunin gidajen da ake kira da Westmore House, Stanwix, Carlisle na ƙasar Ingila. Kada ka ga farincikin da ya lulluɓe fuskar mahaifiyarsa mai suna B.F Richards. Wata rana, kamar yadda Farfesan ya labarta min, ta taɓa kallon sa cikin tausayi da sanyin murya ta ce ma sa, Na san ba zan ga ƙuruciyarka ba sanadiyyar wannan rashin lafiyar taka ba za ta bar ka girma ba. Za ka mutu. Amma fa Idan kana son ganin mace mai raayin kanta yar yankin Yorkshire na Ingila, to Idan ka same ta ka shafa Fatiha. 

Ba a gama yi wa mutum halitta har sai ya koma ga Mahaliccinsa. A wajejen shekarar 2015, sai jin daɗin rayuwar Farfesan ya samu tuntuɓe, tuntuɓen da ya canja masa rayuwarsa kacokan. Wata rana, a gidansa a Maiduguri, kwatsam! sai ya yanke jiki ya faɗi. Ba a yi wata-wata ba aka garzaya da shi Asibitin Jamiar Maiduguri da ake kira da University Hospital, Maiduguri da karaya a kwankwasonsa. Daga baya da abun ya ci tura, dai sai a ka mayar da shi UK a ka ba shi gado a asibitin da ake kira da St Lukes Hospital, wanda yake a keɓantaccen waje ne domin bayar da kulawa ta musamman ga marasa lafiya a wajen birnin Oxford.
Zuwa wannan lokacin, na zama yar gida, saboda yawan kiran sa da nake yi a waya har maɗosanan ƙwaƙwalwata da dodon kunnuwana suka saba da jin kalmomi irin su ba ta kusa, amma za ki iya barin saƙon murya-na-kar ta kwana, wato voicemail kafin a damƙa masa wayar mu yi magana. Hakan na faruwa ne duk yayin da na kira lambar yarsa mai suna Anita da nake kira Idan Ina son jin ya jikin nasa, ko wani abu mai kama da hakan. Ina daga cikin masu kai masa ziyara a kai-a kai da suka ha]ar da yarsa Anita, da kuma wata ɗalibarsa tun a Jamiar Maiduguri, wato UNIMAID, da yanzu take da zama a UK, da kuma mijinta mai suna Andy. 

Na sa an gyara ni ne tsaf saboda Ina tsammanin zuwan ki. Haka ya faɗa wata rana da na kai masa ziyara takanas ta Kano daga Landan. A lokacin, na same shi kan sa a kashingiɗe a kan wani filo mai taushi, ƙasa kuma wani zanin gado ne ruwan hoda da aka ƙawata da hoton zuciya. Gashin kansa kuwa a taje luf-luf da shi, gwanin shaawa ya kwanta gefe guda luf-luf da shi kamar na Balarabe. 

Ba tare da ɓata lokaci ba, ya fara harhaɗowa da tattaro zarurrukan labaransa. Daga wancan gwauron, yana kai su ga mari da sassarfa yana saƙa su. Kamar dai yadda aka saba, labaran nasa ba su wuce na yadda mayaƙan sari-ka-noƙe na Boko Haram suka yi wa sojojin Najeriya kwantan ɓauna ba a kan hanyar dawowar su daga Chibok. Sai ya gangaro ga yadda shahararren mai kuɗin nan na Nahiyar Afirka, wato Aliko Ɗangote ya zama wanda ya fi kowa arziki a Afirka. Sai ya cake a abawar zaren labarin nasa na ƙarshe da gudunmowar da birnin Birmingham na ƙasar Ingila ya taka wajen juyin-juya halin bunƙasar masanaantu a Duniya. Bayan wasu yan mintina, sai ya saki wani gwauron numfashi, ya yi mamul-mamul da baki, tare da miƙar da fuskarsa domin ta ɗan sarara. Lallai rai dangin goro ne sai da ban iska. A lokacin, babu abunda ka ke ji a ɗakin banda ƙi-ƙi-ƙi da kiirrr-ƙiirrr ɗin ƙararrakin sawayen tayoyin abun kai wa marasa lafiya abinci zuwa ɗakunan su a siririyar hanyar da za ta kai ka ga ɗakin nasa.

Akasarin mutane, yayin da shekaru suka dankwafar da dugadugansu, tsufa kuma ya ranƙwafar da bayansu, gigin tsufa kuma ya lulluɓe su da bargunan nan nasa masu kauri da nauyi, sai su fara rikirkicewa. Haka nan, sai su kasa bambance da mayyaze abubuwa. Za ka iya cewa shi Farfesa ya turmuza hancin rikicin tsufansa har ƙas. A ƙarshe-ƙarshen shekarun rayuwarmu da shi, na yi mamaki da na ga yadda Farfesa ba ya cakuɗa abubuwan da ya sani ko ya yi muamala da su ko kuma ya riska. Tun daga kan mutane, da gurare, da kuma shekarun da ya rayu a cikinsu. Wasu lokutan, kawai sai na ga ya ƙura min idanu har tsawon wani lokaci. Can kuma sai ya saki murmushi, ya ce, Kin gan ki kin girma! Kamar ba ke ce yar ƙaramar yarinyar nan ba da kya jin tsoron hawa jirgin ƙasa a tashar ‘Charing Cross’ ba! Ko kuma ka ga ya ɗauki tsawon mintuna ashirin yana kallon da nazarin lakcar da aka yi wa su yarsa Anita a Jamia a kan ilimin kimiyyar sararin samaniya ta amfani da naurorin jiyo sautuka, wato Radio-Astronomy da kuma kisfewar wata da ake kira da Lunar Eclipse. Can kuma, sai ka ga ya shimfiɗar da gaban tafukan hannayensa a kan ƙirjinsa kamar mai yin ƙabalu, sai kuma ya ce, Anita za ta ba ki wasu takardu idan kin koma Ingila. 

Daga baya, sai ya fara ba ni sababbin labaran da bai ba ni su ba a da. Amma fa waɗannan labaran sun fi na farko da ya ba ni saurin karya zuciya ko saka muryar Farfesan ta dinga raurawa, kamar zai yi kuka saboda abubuwan da suke tuna masa da kuma dukansa da suke yi. Tun daga yadda aka ƙi ɗaukar sa aikin soja yayin Yaƙin Duniya na biyu, da tsimin mazan jiya da yake ji har yanzu domin shiga ƙaramin aikin soja na gida da ake kira da Home guard. Da kuma yadda aka ci amanar Birtaniya da yadda ta faɗa tsaka mai wuya na barin ta ita kaɗai a bakin ruwan Calais a yaƙin Duniya na Biyu. A lokacin, dukkanin mu mun ɗaure jakunkunanmu a dogayen fala-falai da wani abu da muke kira da ‘scythes’, kowannenmu na manne da bindigarsa ta harbi-ka-ruga. Hitler, a lokacin yana ganin kamar ya ci mu da yaƙi ya gama! Ya hakaito. 

Maimakon tsufansa ya raunana yadda yake gani da tunanin abubuwa, sai hakan ya akkasu a gare shi. Shi ɗin nan dai da ka samu tun kafin yawan shekaru sun ranƙwafar da dugadugansa da maɗigarsa, shi ne dai. Za ka gane hakan ne Idan ka kalli cikin ƙwayar idonsa, ka kuma ga yadda yake sarrafa doron tsinin yan yatsunsa. 

Abunda ya kaɗa min hantar cikina shi ne, lokacin da na yi mafarki ana gwabza Yaƙin Duniya na Biyu da ni a ƙasar Isfaniya, wato ‘Spain’. Sai kawai na tsince kaina a rundunar Hitler, da ake wa kirari da mayaƙin zamba. Sai ya cigaba da labarta min cewa, a lokacin da ya yi ɓad-da-kama ya shige cikin sojojin Hitler da har ta kai ga ya yi musu romon baka ya jagoranci wata rundunar sojojin sama zuwa ga Ingila da aka yi musu kwanton ɓauna, a kame su. Na shirya waɗannan dabarun ne duka fa a mafarki. A inda na ringa kaɗa kuben yaƙi domin sojojin Ingila su ji, su zo su cafke su. Ya furta cikin nusawa cikin tunani. Amma fa waɗannan dukansu a cikin mafarki suka faru. Sai na ga ya miƙo hannunsa ya kama nawa. Shin yaƙin Duniya na biyu ya kusa zuwa ƙarshe, a lokacin da mayaƙan Boko Haram ke ƙara kutsawa cikin birnin Maiduguri, ko kuma dai ƙarar jiragen saman Jamusawa ne ke shawagi a sararin samaniyar garin Oxford don yin aman wuta ga babbar birni kuma zuciyar masanaantu na Coventry dake a tsakiyar yammacin Ingila? Kai ka ce waftar nan ce da hannun Malaika Azrailu ke yi wa rai Idan ya keta sararin samaniya. 

A waɗannan lokutan da tafiyar gobe-yau-jiya ke gudana, wato Time Travel ga tunanin Farfesan, a lokaci guda kuma jasadinsa da ruhinsa suka kasa mayyaze da bambance shin har yanzu a cikin Saharar Maiduguri suke ko kuma a katafaren gurin da ake kira da Queens College Oxford dake a Jamiar Oxford suke. Sai ya cigaba da sambatun sa kamar haka: Maimakon na bi ta ƙofofin zinare da azurfah na Aljannah, kullum abunda na fi so sama da hakan shi ne na roƙi alfarmar St Paul ko zan iya zama kusa da shi na ɗan wani lokaci ko na samu tabarrakinsa yayin da burujin Duniyar da nake ciki ke cigaba da jujjuyawa…. Sai da yayi gyaran murya sau biyu kafin ya ajiye ƙarshen maganar tasa da cewa, Daga nan kuma sai na zuba wa sarautar Allah ido na ga mai zai faru da ni. 

Sai kuma ya ƙara cigaba da saƙa zaren labarin nasa na farko kamar haka: ko kuma, sai ya ɗago kansa ya kalle ni da giransa a tashe da ƙwayoyin idanuwansa masu haske da kana kalla, ka san rashin lafiya ta ziyarce su, ya ɗora da faɗin, Ko kuma kai tsaye na zarce ga Ubangiji na roƙe shi ko zan iya samun a yi min Duniya ta ni kaɗai, wato ‘Planet’. Zan nemi hakan ne saboda na samu damar yin bincike-bincike da gwaje-gwaje na kimiyya. 

Bayan shafe shekara guda cur yana jinya a asibitin St Luke na birnin Oxford, sai ya tayar da borin sai an dawo da shi Najeriya. Hakan ya faru ne sanadiyyar ƙawazuci da bege da ya cika shi na dawowa ƙasar domin ya kammala ayyukansa da sauran bincike-bincikensa. Wato projects-projects ɗinsa da bai ƙarasa ba. A lokacin ofishin hulɗar jakadancin Birtaniya da ƙasashen waje, wato Foreign Office yana gargaɗin duka mazauna Birtaniyar a kan guje wa tafiya zuwa jihar Borno saboda haɗarin hakan. Amma hakan bai tanƙwara niyyar Farfesan ba na fasa dawowa jihar Maidugurin. 

Lokacin da ya sauka a garin a watan Nuwambar shekarar 2016 a keken tura marasa lafiya aka kawo shi, saboda raunin da jikin nasa ya yi. Komai mai yiwuwa ne a wajen Farfesa, bai san wata kalma wai ita mara yiwuwa ba a ƙamus ɗinsa. Haka Maryam, wato tsohuwar ɗalibarsa ta furta yayin da zuciyarta take cike da alhini, muryarta cikin raurawa da tausayi. A daren da ya sauka a Maidugurin, Sule ya kira ni, yana shaida min cewa Farfesa ya galabaita, amma duk da hakan, bakinsa har yanzu yana jin daɗin ɗanɗanon abincin da yafi so, wato farfesun hantar kaza. 

Himma ba ta ga rago! Da wayewar gari, sai Farfesan da mai kula da shi, wato Sule suka fara sababbin shirye-shirye na yadda za su kammala gagarumin aikinsu na dasa bishiyoyin gida a faɗin yankin Maidugurin. Sunan project ɗin nasu, Indigenous Trees Project.

Tabbacen abu ne, cewa dukkanin rubututtukan taaziya na ƙarewa ne da abu iri ɗaya, wato:  Farfesa Richard ya riga mu gidan gaskiya a yau 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2016 a jihar Maiduguri. Ya rasun ne gajeriyar jinya da ya yi. Ya mutu ya bar ɗan uwansa da ake kira da Martian, da kuma yarsa Anita. 

Duk da yawan tattaunawar da na yi da shi da kuma ]imbin bayanan da ya ba ni game da shi da rayuwar sa, har yanzu lankafaffun takardun da na ware na ɗaukar shiftar bayanansa da kuma shekararsa ta ƙarshe a Oxford har yanzu takardun ban cika su ba. Lokacin da na tsara zan ware watan Janairu domin rubuta marsiyyar Farfesan, wato taaziyyarsa, na yi tunanin nan da nan zan yi na gama. Ina ganin tunda Farfesan ya riga mu gidan gaskiya kuma ba na ganin sa da idanuwana na zahiri kamar zan fi samun damar sanin haƙiƙarsa da kuma ayyukan da ya yi a rayuwarsa.

A wannan bazarar ne tafiya ta ƙara kama ni zuwa Maidugurin domin bincike mai alaƙa da karatuna. Shekaru takwas kenan da zuwana jihar Maidugurin; wanda ya zo daidai da watanni shida da rasuwar Farfesa. Har yanzu surar hotonsa babba na kafe a bangon falonsa a ƙasan wannan kujerar tasa da yake ji da ita. An gudanar da janaizar tasa ne a tsakiyar muku-mukun sanyi, lokacin da busasshiyar Iskar Sahara ke kaɗawa da busawa tsakankanin masu gudanar da janaizar tasa wacce ta samu halartar mutane ɗaruruwa. Yaba kyauta, tukuici. Inji Mallam Bahaushe. Gudunmowar da Farfesan ya bayar ne ya sanya Jamiar Maidugurin da ya koyar na tsawon shekaru suka sadaukar da dashen bishiyoyin da ya assasa gare shi ta hanyar bayar da isasshen filin da za a daddasa su. Hakan ce ta sanya Sulen ya gusa daga gidan Farfesan da yake zaune da iyalansa zuwa ƙarshen katangar Jamiar.  Ya yi hakan ne domin samun sauƙi wajen kulawa da bishiyoyin da suka dasa guda dubu ashirin (20,000) kafin Farfesan ya riga mu gidan gaskiya. 

Amma waɗannan abubuwan na sama kamar inuwarsa ne, ko kuma sadaƙatul jariyah da ya bari a Duniya. Watarana, Ina cikin duba sunayen dake kan Wasaf ɗi na, sai na ga ashe sunan Farfesan na daga sunayen da nake Wasaf da su. Wani hotonsa ne a kan shafin nasa yana kallon sararin samaniya a lokacin da saman ta yi shuɗiya kamar wacce aka zana; gwanin shaawa. 

Na tuttura wa mutanensa da hotunansa a lokacin da ya yi wata tafiya a ƙaramin jirgin ruwa a Dam ɗin da ake kira da Alam da yake a Tafkin Chadi a shekarar 2009. Wannan hoton ne babbar yar Sule da ake kira da Zainab ta saka a matsayin hoton shafin  Wasaf ɗin ta. 

Da na ga babu wani ƙwaƙƙwaran dalili da zai sa na cigaba da zama a Maidugurin, sai zakara ya ba ni saa na hau jirgi, sai Birnin Sarauniya, wanda mu a can muke wa kirari da Queens. Daga baya ne ya bayyana gare ni cewa, akwai bayanan Farfesan a kundin adana bayanan tsofaffin ɗalibai na Jamiar ta Oxford ɗin da ake kira da College archive. Hakan ya faru ne wata rana bayan na yi wa sakatariyar kula da sashin adana bayanan tsofaffin ɗaliban mai suna Jen. Kayan nama ba ya kashe kura. A wannan rumbun, na san zan iya yin tsintuwar zarurrukan da zan ƙwarara saƙar da na yi ta rayuwar Farfesan da zarurrukan da na san kaurinsu da  ƙwarinsu ba su kai wanda zan ci karo da su a rumbun ba. Tsahon ran rayukan labarurrukan da ya labarta min na rayuwarsa da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar tasa ya kai wajen shekaru 900 Idan ka ja gezarsu ka kuma tufke su a marin da ka fara saƙar tasu daga nan. Jirgin ƙasa na hau mai zuwa Oxford.

Na haɗu da sakatariya Jen ne a wani ofishi mai rufin sili dogo kamar zanƙalaƙoƙi dake da kusurwa huɗu dake kallon lambun da ake kira da Provost Garden, wato shugaban kwaleji dake ƙarƙashin Jamiar Oxford. Idan ka ƙura wa bishiyoyin dake cikin lambun na-mujiya, ka kuma wurga maganan naka dai har ila yau ga gilasan dake maƙwabtaka da bishiyoyin, sai ka yi tunanin kamar auren zobe ne tsakanin bishiyoyin da suka baibaye lambun da kuma gilasan da suke kallon sa waɗanda sun kai shekaru 100 da wannan aure! Da muka shiga, sai Jen ta miƙo min kundin adana bayanan ɗaliban shekarar 1940. Ga hotonsa sanye da irin rigar nan jacket da ake fi saƙa ta a ƙasar Scotland.

Duk da hotonsa nasa baƙi da fari ne; hakan bai hana bayyana kalar shuɗayen ƙwayoyin idanuwansa ba da Turawa ke wa laƙabi da ‘pale blue eyes’. Wani ɗan gajeren bayani a kansa ya bayyana addininsa da wani addini mai suna CofE. Haka kuma shi ne ya lashe lambar yabo daraja ta ɗaya a gasar baje kolin fasaha da aka yi mai suna Riggie Exhibition lokacin yana aji biyu a Jamiar.  Har ila yau, ya fita da sakamako mai daraja ta farko, wato first class a lokacin da ya gama digirin sa na farko a ɓangaren kimiyyar rayuwar dabbobi da ake kira da ‘Zoology’ a shekarar 1942. A cikin shekara uku kacal, ya kammala digirinsa na uku, lokacin ba a fi wata uku da ayyana samun zaman lafiya a Nahiyar Turai ba. A cikin kundin adana bayanan ɗalibai a ƙasan gurin da aka rubuta Academic Distinctions, College Offices, Sports and Athletics babu komai. Wajen da ake rubuta sanaar ɗalibi shi ma ba a zayyana komai a wajen ba. 

Saboda karamci, sai ta nemi da ta yi min kwafe na shafin dake ɗauke da bayanan Farfesan, ta kuma ba ni shawarar da na tuntuɓi iyalan Farfesan domin samun ƙarin bayanai a kansa, ko kuma na tuntuɓi wacce ta gada, wacce yanzu ita ce jami’ar sadarwa ta kwalejin. Ta taimaka wajen buga tarihin rayuwar Farfesan da ya rubuta da kansa da ya kira da Queens at War a mujallar  kwalejin da kwalejin take wallafawa da a shekarar 2010 bayan dawowa ta daga Maidugurin (alal haƙiƙa wannan rubutun da aka buga a College Magazine su ne waɗanda na rubuta daga shiftar da ya yi min ina rubutawa, kuma su ne wasu daga shafukan da ba a samu damar tattara su ba da yar wajensa Anita ta turo min bayan rasuwarsa.) Sai na ga hanya ta ɓace min a dogon kwararon da muka biyo da kuma wasu hanyoyin da a da na bi su na tsohuwar kwalejin tawa. Da na ƙwanƙwasa farar ƙofar ofishin Mista Emily, sai ƙwaƙwalwata ta harbo min hotonta da duk lokacin da na zo karanta Mujallar Kwalejin nake yin tozali da ita Idan na kalli shafin bangon jaridar na baya. Sai na gan ta jin ta ya fi ganin ta. Kodayake dai yadda take tsaga dogon gashin kanta ya kwanta gwanin shaawa, dole ya ba wa mai kallo shaawa. Sai na same ta har yanzu wushiryarta na nan ɗaras a tsakankanin fararen haƙoranta reras da su. 

Mutuwa rigar kowa! Shi ne Uba a duk lokacin da za a yi wani taro a kwalejin nan, ya girmi kowa…. ta furta cikin alhini, muryarta sanyaye.

Yadda take bayani a kan Farfesan za ka iya cewa ba wani tuna shi sosai da sosai ta yi ba, yadda ya kamata. Haka nan idan ka nutsu sosai sai ka ga kamar Inuwarsa ta gani kawai ba gangar jikinsa ba. A lokacin da nake fitowa daga ɗan ƙaramin ofishihnta wanda wata bishiya mai faka-fakan fararen fure masu danƙo idan ka kai hannu gare su, da ake wa laƙabi da magnolia tree. Na ɗaraso zuwa inda na haɗu da sakatariya Jen. Sai na ji kamar ba ta biya ni ba. Ba ta biya ni ba mana! Kamata ya yi a ce a matsayinta na tsohuwar mai adana bayanan tsofaffin ɗaliban kwalejin dake ƙarƙashin kulawar Jamiar Oxford ta tuna tare da baje min zare da abawa a kan Shehin Malamin, amma sai ya zamanto ga abawar a hannunta riƙe, amma ta kasa lalubo zaren da za ta saƙa min saƙar rayuwar wannan bawan Allah da ya bar mahaifarsa ya shiga Sahara domin canza rayuwar wasu mutanen da Annabi Adamu ne kaɗai ya haɗa su a nasaba. Ba dangin iya ba ko na Baba! Na samu wasu ƙarin bayanai a kan Farfesan a wajen shugaban  Kwalejin, duk dai shi ma ba wasu bayanai ba ne da za a yi ta-kanas-ta Kano domin zuwa safararsu ba, amma dai sun taimaka. Amma duk da waɗannan ƙarin bayanan da na samu daga shugaban kwalejin, hakan bai ƙara min haske ga sanin da na yi wa shi Shehin Malamin ba. Farfesan Farfesosi. Zaki ba ka fargaba. Gwanki sa gabanka inda ka ke so. Fari mai farar aniya. Farin Bature na farar Sarauniya! 

A wannan ranar a Oxford ne na kunce dukkanin saƙar zarurrukan labaran da Farfesa ya ba ni a kansa dangane da rayuwarsa, haka kuma na dinga bi ina feɗe darussan dake cikin rayuwar tasa har wutsiya: tun daga ranar da wayar salula ta ta yi rauji yayin da ya kira ni ta wayar tawa Ina saman ɗakin benen gidanmu, zuwa yadda muka dinga haɗuwa da shi a Farmers Club, sannan na gangaro yadda muka shafe wata guda cur ni da shi a Maiduguri a gidansa yayin da taurari suka ƙawata sararin samaniya yana saƙa min zarurrukan labaran gwagwarmayarsa ni kuma Ina tufkewa.

Ba wai tsuran labarurrukan rayuwar tasa ba ne abunda na hakaito daga shi ɗin ne babban darusan da na koya ba, a’a, zaman da na yi da shi ne da abubuwan da na gani ne da idanuwana a ƙarshe-ƙarshen rayuwar tasa ne abubuwan da suka fi taɓa ni. Zuciya takan iya manta sautukan da ta ji ta fatun kunnuwa, amma da wahala ta sha’afa ga abubuwan da suka faru da ita na kyautatawa ko akasin hakan. Daga cikin irin waɗannan waƙi’an, abubuwan da suka faru sun haɗar da gudunmowarsa da ya aiko lokacin bikin Miss Emily ta wani ƙayataccen zanin gadon da aka yi da kaɗaɗɗiyar farar tausasassar audugar ƙasar Masar tun daga Maiduguri har Birnin Oxford. Haka nan da yadda yana kan gado a asibiti a Headington ya ringa shiftar wasiƙa ga babbar jaridar nan ta ƙasar Ingila da ake kira da Guardian mai taken a home of rest for dictators, wanda a cikinta ne ya bayyana min yaya ma sunan jirgin ruwan da Napoleon ya yi amfani da shi a ƙarni na 18 yayin mamayar Nahiyar Turai. Kai har ma da yadda ya tattaka matattakalar bene mai hawa 90 yayin shiga kallon wani babban fim a kan kimiyyar almara da ake kira da sci-fi film Silimar da ake kira da Marble Arch Odeon da muka je tare shekaru biyu da suka wuce. Kai! fim ɗin ya ja ni sosai, ya faɗa yayin da aka fara taken lamba, kawai dai duk lokacin da suka samu saɓani, sai su kaure da faɗa. 

Kullum Ina kwatanta sanin da na yi wa Farfesa tamkar labarin makafin nan ne guda huɗu da kowannen su ya siffanta giwa da iya kaɗai sashin jikinta da ya taɓa. Duk ƙoƙarin da na yi don na zayyana rayuwarsa a haƙiƙar yadda take a cikin waɗannan shafukan da ke tsakankanin  tafukan hannayenka, hakan ya ci tura. Ta yaya ma hakan za ta kasance? Sanin bawa zahiri da baɗininsa dama ai sai Mahaliccinsa. Rubutuna a kan wannan Shehin Malami a Boko tamkar wanda ya ƙura wa kogi idanu ne yake so ya kama kifaye, zai kama abunda ya kama ne ya gaji ya tafi ba tare da ya kame kifayen kogin duka ba. Amma ni har yanzu Ina gaban kogin ko zan iya cika burgamin nawa kuwa ko kuwa aa.

Wanda ya fassara ƙasidar shi ne, Mudassir S. Abdullahi, ɗalibi a Jamiar Bayero da ke Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *