‘Yan bindiga sun saki mahaifiyar Rarara bayan shafe kwanaki a tsare

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Masu garkuwa da mutane sun saki mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara.

Blueprint Manhaja ta rawaito cewa ‘yan bindiga dake satar mutane don neman kuɗin fansa sun yi garkuwa da Hajiya Hauwa Adamu a gidanta a ranar 28 ga watan Yuni, 2024, a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, lamarin da ya haifar da damuwa da cece kuce a tsakanin masoya fitaccen mawaƙin musamman a arewacin ƙasar nan.

Tun da farko dai masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su maƙudan kuɗin fansa Naira miliyan 900, kawo yanzu ba mu iya tabbatar da ko an biya kuɗin ba kafin sakin dattijuwar mai shekara 75.

A cikin wani sabon bidiyo da Rarara ya wallafa a shafinsa na TikTok da Instagram a safiyar yau Laraba, an ga yadda ya saka  bodiyo da hotunan mahaifiyar ta sa wadda akwai alamar gajiya a tattare da ita.

Mawaƙin ya kuma nuna godiyarsa ga Allah S W A da ya sake haɗa shi da mahaifiyar ta sa bayan da tashe kwanaki a hannun ‘yan bindiga.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! cikin yarda da amincin ubangiji mun samu dawowar mama cikin amincin”.

Kazalika, Rarara ya kuma miƙa godiyarsa ga masoyansa, abokan sana’a da ma duk waɗanda suka jajanta masa game da lamarin.

“Ina matuƙar godiya ga Ubangiji na, ina godiya ga ‘yan uwa da abokan sana’a ta, ina godiya ga masoya na, na duk duniya baki ɗaya. Inji Rarara. Inji fitaccen mawaƙin.

By ukarofi