‘Yan bindiga sun tare hanyoyin ofisoshin sabbin kantomomin Ribas da yin harbe-harbe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An samun harbe-harben bindigogi a ƙananan hukumomi da dama na Ribas bayan da wasu ƴan daba suka yi yunƙurin hana sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a jihar shiga ofisoshinsu.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin da hukumar zaɓen jihar, RSIEC ta yi a ranar Lahadi.

Bayan zaɓen ne, Gwamnan jihar, Siminialayi Fubara ya rantsar da kantomomin baki ɗaya na ƙananan hukumomi 23 da ke jihar.

A sakamakon haka ne, Sufeton ƴan sanda, ta hannun kakakin ƴan sandan jihar, Grace Iringe-Koko ya umarci jami’ansu su fice daga duka ofisoshin ƙananan hukumomin jihar.

Rahotonni sun bayyana cewa, a safiyar ranar Litinin ne wata ƙungiyar siyasa da ba ta amince da sakamakon zaɓen ba, ta shirya matasa guda ashirin a kowacce gunduma don tare hanyoyin da zai kai kantomomin sakatariyar ƙananan hukumominsu.

Ana cigaba da zaman ɗar-ɗar kasancewar an samu harbe-harbe a wurare da dama na faɗin jihar.

By Babaji